Amarya ta yiwa Angonta kyautan jirgin ruwa mai tsada ranar daurin aurensu

Amarya ta yiwa Angonta kyautan jirgin ruwa mai tsada ranar daurin aurensu

  • Wata hamshakiyar Amarya ta bawa jama'a mamaki bisa gagarumin kyautar da ta yiwa Angonta ranar aure
  • Yayinda aka daura auren, Amaryar ta bayyana cewa ta saya masa jirgin ruwan zamani don shakatawa
  • Amaryar tace ta rasa abinda zata sayawa masoyinta ne yasa ta saya masa abin hawan

Wata kyakkyawar Amarya ta tada kura yayinda ta baiwa Angonta kyautan sabon jirgin ruwan zamani.

Wannan abu ya faru ne a birnin Miami dake kasar Amurka.

A bidiyon da aka daura kan Instagram, Amaryar ta yi sanarwar ne lokacin da Limamin coci ya daura aurensu.

Amarya ta yiwa Angonta kyautan jirgin ruwa
Amarya ta yiwa Angonta kyautan jirgin ruwa mai tsada ranar daurin aurensu Hoto: @morganscottfilms
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalilin da yasa ta bashi kyautar jirgin ruwa

A cewar Amaryar, ta na son baiwa Angon abinda bai da shi ne kuma bayan binciken da ta gudanar, ta gano bai da jirgin ruwa.

Kara karanta wannan

Ba zan sake Zina ba sai Allah ya bani miji, Jarumar Nollywood

Ta bayyana cewa ta yi hakan ne don nuna godiyarta bisa shirya musu bikin aure mai gamsarwa.

Mijin shima ya nuna farin cikinsa inda ya rungumi matarsa.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel