Boko Haram ta saki hotunan ɗan sanda da ma'aikatan gwamnati da ta sace a Borno

Boko Haram ta saki hotunan ɗan sanda da ma'aikatan gwamnati da ta sace a Borno

  • Kungiyar Boko Haram ta fitar da hoton jami'in dan sanda da ma'aikatan gwamnatin Borno da ta sace
  • Yan ta'addan sun sace ma'aikatan ne yayin da suke kula da aikin ginin titi a kauyen Wovi kan hanyar Chibok zuwa Damboa
  • Duk da Rundunar Sojojin Najeriya ta sha nanata cewa ta ci galaba a kan yan ta'ddan, a na cigaba da samun hare-hare a yankin

Borno - Kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ta fitar da hotunan mutane uku cikin wadanda ta sace a hanyar Chibok zuwa Damboa a jihar Borno a kwana-kwanan nan, SaharaReporters ta ruwaito.

A makon da ta gabata ne kungiyar ta sace wasu ma'aikatan Hukumar Ayyuka na Jihar Borno da ke aiki a kauyen Wovi.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi

Boko Haram ta saki hotunan 'yan sanda da ma'aikatan gwamnati da ta sace a Borno
Hotunan wasu daga cikin wadanda Boko Haram suka sace a Borno. Hoto: SaharaReporters
Asali: Facebook

Wadanda aka sace din suna sa ido ne a kan aikin ginin titi mai nisan kilomita 45, kafin yan ta'addan suka sace su tare da motocci uku kirar Hilux duk suka yi cikin Dajin Sambisa da su.

Sai dai, daya daga cikin ma'aikatan ya tsira da lafiyarsa.

A cikin makon, kungiyar ta fitar da hotuna daban-daban na yadda suka sace ma'aikatan a wurin.

Ta kuma fitar da hoton wani dan sanda da wasu mutane biyu cikin wadanda suka sace.

Tun bayan mutuwar tsohon shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ISWAP na cigaba da mamaye garuruwa a yankin Tafkin Chadi, rahoton SaharaReporters.

A baya bayan nan, ta nada Wali Sani Shuwaram, wani dan shekara 45 a matsayin sabon shugabanta na yankin Tafkin Chadi.

Kungiyar ta samu karin mambobi da suka tsere daga bangaren Shekau suka koma ISWAP.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Ma'aikatan Npower sun fito zanga-zanga a Abuja kan rashin biyansu alawus

Rundunar sojojin Najeriya ta dade tana nanata cewa ta ci galaba kan yan ta'addan sai dai har yanzu a kan samu hare-hare a yankin.

Kungiyar yan ta'addan sun yi sanadin mutuwar fiye da mutane 50,000 da raba miliyoyi da muhallinsu musamman a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

A baya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.

Kara karanta wannan

Jihar Niger: 'Yan bindiga na karbar sigari da wiwi a matsayin kudin fansa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel