An nada shugaba Buhari shugabancin wata babbar kungiya a Afrika ta PAGGW

An nada shugaba Buhari shugabancin wata babbar kungiya a Afrika ta PAGGW

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zama shugaban kungiyar PAGGW a Afrika yayin gudanar da wani taro a Abuja
  • An gudanar da taron ne a ranar 2 ga watan Disamba a Abuja, inda aka mika ragamar kungiyar ga Buhari da Najeriya
  • A cikin wata sanarwar da aka fitar, an bayyana yadda Najeriya da shugaba Buhari za su kawo sauyi a kungiyar ta PAGGW

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi ragamar shugabancin kungiyar Pan African Great Green Wall (PAGGW), a Afirka, kamar yadda karamar minista a ma'aikatar muhalli, Mrs Sharon Ikeazor, ta sanar a ranar Lahadi a Abuja.

Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Sagir el Mohammed ya fitar ta ce Najeriya ta karbi ragamar mulkin ne a karshen taron shugabannin kasashe da gwamnatocin PAGGW karo na 4 da aka gudanar a ranar 2 ga watan Disamba a Abuja.

Kara karanta wannan

An gano abin da Buhari ya fadawa Shugaban kasar Afrika ta Kudu kafin ya lula zuwa Dubai

Minista Sharon Ikeazor kan batun Buhari
An nada shugaba Buhari shugabancin wata babbar kungiya a Afrika ta PAGGW | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

A cewar ministar:

“A karshen taro na 4 na CHSG, Najeriya ta karbi shugabancin kungiyar PAGGW.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Don haka nan da shekaru biyu masu zuwa, Najeriya da Shugaba Buhari za su kasance shugabannin kungiyar ‘Great Green Wall Initiative’ a Afirka.
“Wannan na nufin cewa a cikin wannan lokacin, Najeriya za ta yi aiki tukuru don magance matsalolin zaizayewar kasa, samar da abinci, kwararowar hamada, sauyin yanayi, raguwar yanayin dazuzzuka da rayayyun halittu a Afirka da dai sauransu.
"Tare da jajircewa mara misaltuwa da shugaban kasa ya yi wajen magance matsalolin sauyin yanayi da kwararowar hamada, tare da mutuncin da yake dashi a tsakanin kasashen duniya, za a samu nasarori da dama a lokacin mulkinsa."

Misis Ikeazor ta tuno da jajircewar shugaban a taron sauyin yanayi (COP26) da aka gudanar a watan Nuwamba a Glasgow ta kasar Scotland a nahiyar Turai.

Kara karanta wannan

Rikicin Goje da Inuwa: Kotu ta tasa keyar hadimin Goje zuwa kotu saboda yin rubutu a Facebook

Daily Nigerian ta rahoto cewa, ministar ta ce shugaban ya bayyana kyakkyawan fata game da burin Afirka na maido da sama da hekta miliyan 100 na gurbacewar yanayin noma.

The Guardian ta ruwaito to tana bayyana cewa, a jawabinsa na karbar ragamar, shugaban ya bayyana cewa:

"Dukkanin abubuwa daidai suke, za mu karfafa kokarinmu a cikin tattara albarkatu don ci gaba da cimma nasarar shirin saka hannun jari na Decennial Priority Investment Plan (DPIP) 2021-2030 da kuma tabbatar da aiwatar da aikin.
"Gane alkawuran kudi da suka fito a sakamakon "One Planet Summit" da aka gudanar a ranar 11 ga Janairu, 2021 a Paris ta kasar Faransa za a ba shi fifiko mafi mahimmanci.
"Ina so in tabbatar da cewa magance gurbacewar halittu a Afirka da kuma tabbatar da dorewar mutanenmu kan fahimtar illar sauyin yanayi zai karfafa."

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaba a hukumar NEPC

Kara karanta wannan

Shekaru 8 da kashe Sheikh Albani Zaria, an cika masa burinsa na kafa gidan talabijin

A baya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr Ezra Yakusak a matsayin babban direkta/shugaban Hukumar Bunkasa Harkokin Fita da Kayayyaki ta Najeriya (NEPC).

Babban Mataimakin Shugaban Kasa na musamman a bangaren watsa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook.

Shehu ya ce an nada Dr Ezra Yakusak ne a karon farko na wa'addin shekaru hudu kamar yadda ya ke a sashi na 7 (1) a dokar kafa NEPC ta shekarar 1987.

Asali: Legit.ng

Online view pixel