Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaba a hukumar NEPC

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaba a hukumar NEPC

  • Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr Ezra Yakusak a matsayin shugaban NEPC
  • Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar
  • Shehu ya ce nadin da aka yi wa Yakusak ya yi dai-dai da tanadin sashi na 7 (1) na dokar NEPC (Kafa), 1987

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr Ezra Yakusak a matsayin babban direkta/shugaban Hukumar Bunkasa Harkokin Fita da Kayayyaki ta Najeriya (NEPC).

Babban Mataimakin Shugaban Kasa na musamman a bangaren watsa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaba a hukumar NEPC
Shugaba Buhari ya nada sabon shugaba a hukumar NEPC. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya gana da Fasto Tunde Bakare a fadar shugaban kasa

Shehu ya ce an nada Dr Ezra Yakusak ne a karon farko na wa'addin shekaru hudu kamar yadda ya ke a sashi na 7 (1) a dokar kafa NEPC ta shekarar 1987.

A ruwayar jaridar Daily Trust, Shehu yace nadin zai fara aiki ne daga ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar 2021.

Ya ce kafin nadinsa, Dr Yakusak, wanda ke da digirin digirgir a bangaren nazarin dokokin kasuwanci daga Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria shine direktan sashin Dabaru da Manufofi na hukumar ta NEPC.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya kuma ce wanda aka yi wa nadin ya taba aiki a matsayin sakatare na kwamitin gudanarwa na hukumar.

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

Tunda farko kun ji cewa, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel