'Yan PDP sun shigo jam'iyyarmu suna bata mana harkoki, inji sabon kwamitin APC

'Yan PDP sun shigo jam'iyyarmu suna bata mana harkoki, inji sabon kwamitin APC

  • 'Yan jam'iyyar APC da suka bijire suka yi sabon kwamitin CEPC sun bayyana dalilin da yasa suka yi hakan
  • A cewarsu, suna kallo akwai masu yiwa jam'iyyar zagon kasa, kuma ta zargi wasu daga mambobin da zama 'yan PDP
  • Matasan sun bayyana cewa, su sune asalin 'yan APC, kuma sun yiwa jam'iyyar hidima sosai tun kafa ta

Abuja - Daya tsagin kwamitin tsare-tsare na taron gangami na musamman (CEPC) a jam’iyyar APC mai mulki a ranar Litinin da ta gabata, ya yi zargin cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP ne.

Kwamitin ya kuma ce suna sanya rigar jam’iyyar APC mai mulki ne kawai don su lalata kudurin jam'iyyar.

Jam'iyyar APC
'Yan PDP sun shigo jam'iyyarmu suna bata mana harkoki, inji sabon kwamitin APC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar Progressive Youth Movement (PYM) ta kaddamar da sabon kwamitin CEPC a Abuja, a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke dan IPOB yayin da tsagerun ke kokarin sace likitoci a jihar Imo

Sai dai kwamitin Buni ya mayar da martani nan take, yana mai cewa matasan ma jam’iyyar bata san su ba, don haka tsageru ne kawai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake mayar da martani, Shugaban sabon kwamitin na CECPC, Prince Mustapha Audu, ya ce matasan ‘ya'ya ne ga jam’iyyar kuma masu dauke da katin rajista kuma sun hidimta mata.

Blueprint ta ruwaito shi yana cewa:

“Abin takaici, mun karanta duk rahotannin da Sanata John Akpanudoedehe ya fitar game da PYM da sabon kwamitin riko. Abin takaici ne a ce shugaba kamar wannan zai soki mutuncinmu."
“Dukkanmu ‘yan kungiyar PYM, wadannan katunan mu na zama mambobi a jam’iyyar APC ne. Dukkanmu ’yan APC ne da muka yi ta gaba daya. Mun yi sadaukarwa ga jam’iyya, mun bayar da yawa amma abin takaici ne wannan labarin da ya fito.

Kara karanta wannan

Rikicin Goje da Inuwa: Kotu ta tasa keyar hadimin Goje zuwa kotu saboda yin rubutu a Facebook

“Haka ne ke faruwa a kullum idan mutum ya fadi gaskiya, idan wani ya ce akwai wani abu a jam’iyyar mu abin kaunarmu, wadanda ke haifar da wadannan al’amura su ne suke bata mana suna, kuma a gaskiya wasu daga cikin wadannan ‘yan PDP ne.
“Sanata Akpanudoedehe ya yi wadannan zarge-zarge a kan matasa da suka yi hidima da yawa; muna cikin APC tun kafin ya zo jam’iyyar.
"Ya taba zama Sanata a jam’iyyar PDP kuma karamin ministan babban birnin tarayya Abuja a karkashin jam’iyyar PDP. Gwamnatocin PDP guda biyu daban-daban.
“To, ta yaya zai san mutanen da ‘yan APC ne. Mun yi aiki tukuru don wannan jam’iyya, mun sadaukar don wannan jam’iyya, mun sadaukar da kanmu! PDP sun yi nasu taron, don haka mu ne abin dariya ga al’umma. Mu matasa, ba mu da inda za mu je.
“Abin da muke cewa shi ne muna son a yi abubuwan da suka dace. Muna son a yi taron gangamin mu na APC, muna son shugabanni masu nagarta, muna son a dama da matasa, kuma muna son mu shiga cikin tsarin, me ye matsalar hakan?”

Kara karanta wannan

Dokpesi: Zai yi wahala APC ta mika mulki a ruwan sanyi idan ta sha kasa yadda Jonathan ya yi

Zan koya wa sauran jam'iyyun siyasa mummunan darasi a 2023, gwamnan Adamawa

A wani labarin, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya ce zai koyar da sauran jam’iyyun siyasa a jihar munanan darrusa a zaben 2023 mai zuwa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Fintiri ya bayyana haka ne a lokacin amincewarsa da kungiyar kansilolin jihar Adamawa a dakin liyafa na gidan gwamnati da ke Yola a ranar Laraba 1 ga watan Disamba.

An jiyo gwamnan jihar Adamawa yana cewa:

"Sun gaza a cikin shekaru hudu da suka samu damar gudanar da mulkin jihar, kuma ba za mu bar su su yaudari jama'armu ba, za mu ci gaba da yin aiki tukuru, mu samar da romon dimokuradiyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel