Allah ya yiwa Na'ibin Limamin jihar Osun, Sheikh Haroon Adediran, rasuwa

Allah ya yiwa Na'ibin Limamin jihar Osun, Sheikh Haroon Adediran, rasuwa

  • Al'ummar jihar Osun sun shiga jimami sakamakon rasuwar babban Malami kuma mataimakin Limamin Osogbo
  • Babban Na'ibin Limanin, Sheikh Haroon Adediran Asunmo Samonigogo, ya rasu yana mai shekaru 87
  • Gwamnan jihar, Gboyega Oyetola, ya yi alhinin rasuwar babban Malamin kuma yayi kalamai masu kyau kansa

Osogbo, jihar Osun - A ranar Laraba, 1 ga watan Disamba, Allah ya yiwa Na'ibin Limamin Osogbo, Sheikh Haroon Adediran Asunmo Samonigogo, rasuwa yana mai shekaru 87.

Legit ta samu labarin cewa marigayin ya rasu ne bayan gajeruwar jinya da yayi.

Punch ta ruwaito cewa an yi masa Jana'izarsa bisa koyarwan addinin Musulunci.

Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, a jawabin da Sakataren yada labaransa, Isma'il Omipidan, ya saki ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar Limamin.

A cewar Gwamnan, marigayi Imam Adediran, mutum ne mai tsoran Allah kuma mai bashi shawari.

Yace:

"Na yi matukar kaduwa bisa samun labarin rasuwar mahaifinmu kuma mataimakin Limamin Osogbo, Sheikh Haroon Adediran Samonigogo. Mutuwarsa babban rashi ne gareni saboda kaman uba ne gareni."
"Zamu yi rashinsa sosai. Allah ya jikansa, ya gafarcesa kuma ya bashi Aljannah Firdaus."

Allah ya yiwa Na'ibin Limamin jihar Osun, Sheikh Haroon Adediran, rasuwa
Allah ya yiwa Na'ibin Limamin jihar Osun, Sheikh Haroon Adediran, rasuwa Hoto: Isma'il Rufa'i
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel