'Yan banga sun jawo 'yan bindiga sun hallaka mazauna a Sokoto, gwamnati ta fusata
- Gwamnatin jihar Sokoto ta dakatar da ayyukan 'yan bangan sa kai a wasu yankunan jihar saboda barnar daukar fansa ta 'yan bindiga
- A baya kadan an samu faruwar hare-haren daukar fansa daga 'yan bindiga a yankunan Illela da Goronya na jihar
- Gwamnati ta yi Allah-wadai tare da bayyana matakin dakatarwa har zuwa lokacin da za a warware matsalar
Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta haramtawa ‘yan bangan sa kai da ake zarginsu da haddasa kashe-kashe a kasuwannin karkara da hare-haren ramuwar gayya daga wasu 'yan bindiga a wasu kananan hukumomin jihar.
Premium Times ta rahoto yadda irin wadannan hare-hare a kananan hukumomin Illela da Goronyo na jihar Sokoto suka yi sanadiyar mutuwar mutane 45.
Bayan faruwar lamarin, Gwamna Aminu Tambuwal ya yi Allah-wadai da ayyukan ’yan bangan sa kai a yankunan, inda ya yi gargadin cewa gwamnati ba za ta amince da rashin bin doka da oda ba.
A ranar Talata, mai magana da yawun Mista Tambuwal, Muhammad Bello, a cikin wata sanarwa, ya ce gwamnati ta haramta kungiyoyin ne a kokarinta na duba ayyukan wadanda ke da alhakin kashe-kashe a yankin gabashin jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana haka ne a yayin wani taron da masu ruwa da tsaki a jihar suka yi.
Taron ya samu halartar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da ‘yan Majalisarsa da shugabannin hukumomin tsaro na jihar da shugabannin kananan hukumomi da hakimai da kuma wasu shugabannin kungiyoyin ‘yan bangan a jihar, inji TCV.
Yankin sanarwar na cewa:
"A kokarin da ake na dakile yawaitar 'yan bindiga da miyagun laifuka da suka addabi yankin gabas da sauran sassan jihar Sokoto, gwamnatin jihar ta haramtawa kungiyoyin ’yan bangan sa kai gudanar da ayyukansu a jihar."
Ga wadanda suka karya dokar haramtawar, gwamnatin jihar ta sanya tarar da ta kai N500,000.
A cewar sanarwar:
"Don haka, duk wanda aka samu da laifin sashe na 4 (a,b,c da d) zai kasance mai laifi kuma zai biya tarar N500,000.00 ko daurin shekaru 14 a gidan yari ko kuma duka biyun; tara da dauri."
Hakazalika, sashi na 5 kuma ya tanadi cewa:
"Duk mutumin da yake A tare da shi a cikin jama’a yana dauke da muggan makamai ko makamai masu linzami, in ba bisa ka’ida ba, to za biya tarar N200,000.00 ko kuma a daure shi a gidan yari na wa'adin shekaru 7 ko duka biyun; tarar da dauri."
Rahoto: 'Yan Zamfara sun shiga damuwa, 'yan bindiga sun fara karbar harajin noma
A wani labarin, harin da ‘yan bindiga suke kai wa a jihar Zamfara ya fara daukar wani sabon salo inda suka fara karbar kudi a wasu kauyuka.
Rahotanni na baya-bayan nan na nuni da cewa a halin yanzu ‘yan bindigar na karbar haraji daga hannun jama’a ta hanyar kafa shingayen kan titi.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa mazauna garin Magami dake karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara sun koka kan tabarbarewar tsaro, inda suka roki gwamnati da ta taimaka ta ceto su daga barnar ‘yan bindiga da suka sanya musu haraji.
Asali: Legit.ng