Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kaduna ta dage dokar datse hanyoyin sadarwa

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kaduna ta dage dokar datse hanyoyin sadarwa

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da ɗage dokar datse hanyoyin sadarwa a wasu kananan hukumomin jihar
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, yace sauran matakan da gwamnati ta ɗauka suna nan daram
  • A baya gwamnatin ta bayyana cewa matakan harda na datse sabis zasu kwashe watanni uku kafin ta sake nazari a kai

Kaduna- Gwamnatin jihar Kaduna ta ɗage dokar hana amfani da hanyoyin sadarwa na watanni uku data saka a wasu kananan hukumomi tun a watan Oktoba.

Dailytrust ta rahoto cewa gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne saboda yawaitar hare-haren yan bindiga a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, shine ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: An harbe kasurgumin dan bindigan da ya jagoranci sace matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

Gwamna Elrufai
Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kaduna ta dage dokar datse hanyoyin sadarwa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Aruwan ya bayyana cewa tuni gwamnati ta baiwa hukumomin dake da alhaki kan lamarin su maida hanyoyin sadarwa a yankunan da abin ya shafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shin dokar ta haifar da sakamako mai kyau?

A kwanakin baya mun kawo muku rahoton cewa hukumomin tsaro sun bukaci gwamnatin Kaduna ta nemi hukumar sadarwa (NCC) ta datse sabis a wasu kananan hukumomin jihar.

Sai dai duk waɗan nan matakan da gwamnatin ta ɗauka, yan bindiga sun cigaba da cin karen su babu babbaka, musamman a baya-bayan nan a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kwamishinan tsaron jihar, Aruwan, yace sauran matakan da aka ɗauka tare da datse sabis kamar, hana amfani da mashin, rufe kasuwannin mako da hana siyar da man fetur a jarkoki suna nan daram.

Ya ake ciki a Katsina

Bayan jihar Kaduna, makociyarta Katsina ta ɗauki kwatan kwacin irin waɗan nan matakan na datse sabis a kananan hukumomin da yan bindiga ke kai hari.

Kara karanta wannan

Masarautar Dansadau ta yi zaman sulhu da kasurgumin dan bindiga, Ali Kachalla

Amma har zuwa yanzun, duk da kiraye-kirayen da ake yi na matsalar da rashin sabis ke haifarwa, bai sa gwamnati ta ɗage dokar ba, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wani labarin na daban kuma Ku gaggauwa kawo miliyan N200m kafin mu bar wurin sabis, yan binidga sun gargaɗi iyalan dan sanda

Yan bindigan da suka sace matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sun nemi iyalan wani ɗan sanda su biya fansa.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun nemi a tattara musu miliyan N200 cikin awanni 6 kafin su bar gurin sabis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel