Wahalhalu 5 da 'yan Najeriya za su shiga idan man fetur ya koma N340, Shehu Sani

Wahalhalu 5 da 'yan Najeriya za su shiga idan man fetur ya koma N340, Shehu Sani

  • Bayan da gwamnatin Buhari tace za ta cire tallafin man fetur, 'yan Najeriya sun shiga damuwa da jin batun
  • Ana hasashen man fetur zai iya haura N300 idan aka cire tallafin, amma gwamnati ta ce za ta ba talakawa tallafin zirga-zirga na N5000
  • Shehu Sani, tsohon sanata daga jihar Kaduna ya bayyana abubuwan da zasu faru idan aka cimma wannan lamari

Kaduna - Sanata Shehu Sani, tsohon sanata daga jihar Kaduna, ya yi magana kan abubuwan da ‘yan Najeriya za su fuskanta idan farashin man fetur ya koma Naira 340 kan kowace lita.

Kalaman Sani sun biyo bayan sanarwar da Babban Manajin Darakta kuma Babban Jami’in NNPC ya yi cewa farashin man fetur na iya cillawa zuwa N320 ko N340 kan kowace lita bayan cire tallafin a shekarar 2022.

Kara karanta wannan

Minista tayi karin-haske kan yadda za a biya talakawa N5000 bayan cire tallafin mai a 2022

Tsohon sanata a Kaduna, Shehu Sani
Manyan wahalhalu 5 da 'yan Najeriya za su shiga idan man fetur ya koma N340, Shehu Sani | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da yake magana a shafinsa na Facebook, tsohon Sanatan ya bayyana abin da zai faru na kunci idan aka fara sayar da fetur a farashi mai tsada.

Yace:

  1. Albashi zai zama mara amfani
  2. Masu gidaje za su kara kudin haya
  3. Makarantu za su kara kudin karata kuma dole ne iyaye su biya
  4. Farashin abinci, sufuri, kudin ruwa da wutar lantarki za su karu

Ko da yake ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, ta ce za a maye gurbin tallafin man da tallafin sufuri na N5000 duk wata ga talakawan Najeriya, Sanata Sani ya ce shirin gwamnati ba zai iya magance “duk wadannan matsalolin ba”.

'Yan Najeriya da dama sun nuna damuwa da rashin gamsuwa da kudurin gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

N200bn zamu rika kashewa a wata wajen rabawa yan Najeriya N5000

A tun farko, gwamnatin tarayya ta ce za ta rika kashe N200 billion a wata wajen rabawa talakawan Najeriya kudi domin rage zafin da cire tallafin mai zai haifar.

Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur zai yi tashin gwauron zabo.

Leadership newspaper ta ruwaito cewa Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan ne ranar Talata, 23 ga Nuwamba 2023 a taron kaddamar da rahoton Bankin Duniya (NDU).

Asali: Legit.ng

Online view pixel