Dattawan Arewa ga Buhari: Kada ka kuskura ka yafewa dan awaren nan Nnamdi Kanu

Dattawan Arewa ga Buhari: Kada ka kuskura ka yafewa dan awaren nan Nnamdi Kanu

  • Kungiyar dattawan Arewa ta ce sakin shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu zai yi mummunar illa ga bangaren shari’a a Najeriya.
  • Hakan ya biyo bayan bukatar da wasu fitattun shugabannin Igbo suka yi na neman shugaba Buhari ya saki jagoran 'yan aware IPOB
  • Dattawan sun bayyana cewa ya kamata a bar tsarin shari’a ya gudanar da aikinsa akan Nnamdi Kanu ba tare da tsangwama ba

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), a ranar Litinin, 29 ga watan Nuwamba, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi watsi da bukatar wasu fitattun shugabannin Igbo, inda suka bukaci a sako Nnamdi Kanu, shugaban 'yan awaren IPOB.

Kungiyar ta bayyana cewa babu wani dalili na aminci, ingantacce ko kuma sanin makamar amincewa da bukatar, kuma ta shawarci shugaban kasa da kada ya jinkirta bayyana cewa za a bar tsarin shari’a yayi aikinsa akan Kanu.

Kara karanta wannan

An samu sabani tsakanin Minista da Hadimin Buhari kan gwaggwabar kwangilar miliyoyi

Mai magan da yawun dattawan Arewa, Hakim Baba Ahmad
Dattawan Arewa ga Buhari: Kada ka kuskura ka yafewa dan awaren nan Nnamdi Kanu | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Dattawan sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ta, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, kuma Legit.ng ta gani.

Wani bangare na sanarwar ya ce:

“Kungiyar Dattawan Arewa ta yi nazari sosai kan bukatar da dattawan Igbo suka yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari na ya kawo karshen shari’ar da ake yi da Nnamdi Kanu kuma a sake shi ba tare da wani sharadi ba.
“Har ila yau, ta lura da martanin da shugaba Buhari ya bayar wanda dukkansu sun tabo muhimman batutuwan da suka shafi bukatar, da kuma jajircewarsa na yin la’akari da hakan.
“Kungiyar ta ba da shawarar cewa shugaba Buhari zai yi wa kasar rauni wanda tuni ta fuskanci barazanar kalubalen tsaro da yankinta idan ya jinkirta bayyana matakin da ya dace, wanda shi ne a bar tsarin shari’a yayi aikinsa kan Kanu."

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun gargadi Buhari kan yi wa Nnamdi Kanu afuwa, sun bada dalilinsu

Bukatar sakin Nnamdi Kanu babban lamari ne, amma zan yi shawara: Buhari ga Dattawan Igbo

A baya kunji cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sakin Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar yan ta'addan IPOB ya sabawa dokar da ta baiwa sashen Shari'a karfin cin gashin kanta.

Buhari ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin manyan dattawan Igbo wanda ya hada da Tsohon Minista Sufurin Sama kuma tsohon dan majalisa, Chief Mbazulike Amaechi.

Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Buhari yace:

"Ka gabatar da bukata mai wuyan gaske a kaina matsayin Shugaban kasar nan...Tun da na zama shugaba shekaru shida da suka gabata babu wanda zai ce na yi shisshigi cikin aikin Shari'a.
"Wannan bukata na da nauyin gaske. zan yi shawara."

Shugabannin Igbo sun gana da Buhari a fadar Villa

A wani labarin, manyan shugabanni daga yankin kudu maso gabas sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ofishin shugaban kasa da ke fadar Villa, Abuja, a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Aisha Yesufu ga majalisar dokoki: Ku tsige Buhari, har 'yan Arewa sai sun ji dadin haka

Dattijo Hon. Mbazulike Amaechi ne ya jagoranci tawagar wacce ke dauke da tsohon gwamnan jihar Anambra, Dr. Chukwuemeka Ezeife.

Har ila yau a tafiyar akwai mataimakin shugaban kungiyar zaman lafiya na addinai, Bishop Sunday Onuoha, Mista Tagbo Amaechi, da Chief Barr. Goddy Uwazurike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel