An samu sabani tsakanin Minista da Hadimin Buhari kan gwaggwabar kwangilar miliyoyi

An samu sabani tsakanin Minista da Hadimin Buhari kan gwaggwabar kwangilar miliyoyi

  • Hon. Rotimi Ameachi ya kai karar Farfesa Ibrahim Gambari a kan cewa yana yi masa katsalandan
  • Shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasar ya koka ne a kan yadda gwamnati ta bada kwangilar ICTN
  • Hadimin shugaban Najeriyar yace an saba doka, Ministan yace Gambari yana yi masa shisshigi

Abuja - Premium Times tace Ministan sufuri na tarayya, Rotimi Ameachi, ya zargi Farfesa Ibrahim Gambari da shiga shara babu shanu a ma’aikatarsa.

Rotimi Ameachi ya zargi shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da tsoma bakinsa a harkar wata kwangila da hadimin ya bukaci Ministan yayi gaskiya.

Binciken da jaridar tayi ya nuna Ibrahim Gambari ya nemi a bi doka wajen bada kwangilar ICTN ta dakon kayan da aka shigo da su daga waje a tashoshin kasar.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun gargadi Buhari kan yi wa Nnamdi Kanu afuwa, sun bada dalilinsu

Hukumar BPP ta yi korafin cewa ba a bi ka’ida wajen bada kwangilar ba, tace an zakulo kamfanin ne kawai ba tare da an yi takara yadda aka saba ba.

Hadimin shugaban kasa, Ibrahim Gambari ya yi amfani da kukan da BPP ta yi, ya rubuta takarda ya na jan-kunnen Buhari a kan danyen aikin Ministan na sa.

Rotimi Amaechi ya kai karar COS

A watan Oktoban nan, Ameachi ya rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa, yana zargin Gambari da kokarin sa baki a wannan kwangila domin ya samu wani abu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An samu sabani tsakanin Minista da Hadimin Buhari kan gwaggwabar kwangilar miliyoyi
Rotimi Amaechi a taron FEC
Asali: Twitter

Ministan sufurin yace har sai da ‘diyar hadimin shugaban Najeriyar, Bilkisu Gambari ta same shi a kan yadda za a ba mutanensu wannan kwangila mai tsoka.

A takardarsa, Amaechi ya bukaci Gambari ya daina shiga harkar ma’aikatarsa, sannan ya nemi shugaban Najeriya ya amince a karkare batun bada kwangilar.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya yi martani kan fastocinsa dake yawo na takarar shugaban kasa a 2023

Washegari ke da wuya takardar ta isa teburin Muhammadu Buhari, kuma ya bada umarni a bar kamfanonin biyu da aka ce ba su dace ba, su cigaba da aikin.

Mai girma Muhammadu Buhari ya kunyatar da babban hadiminsa, Gambari, inda ya tabbatarwa Ministan sufurin cewa ya ji kukansa, kuma ya yi yadda yake so.

Zuwa yanzu Gambari bai bada wata amsa ba, kuma yunkurin tuntubarsa a wayar salula ta ci tura.

Badakalar kwangilar ICTN?

A baya kun ji yadda wani rahotonmu ya tona yadda shugaban kasa da Ministan na sufuri su ka ba MedTech Scientific Ltd and Rozi Int’l wannan babbar kwangila.

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da dokoki da ka’idojin aiki wajen bada wannan aikin, bayan ta sake dawo da tsarin na ICTN da gwamnatin Jonathan ta soke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel