Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da DPO na yan sanda

Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da DPO na yan sanda

  • DPO na yan sandan Furgar ya shiga hannun masu garkuwa da mutane da suka addabi al'ummar Najeriya
  • Yan bindigan sun tare shi a hanya a watan Nuwamba yayinda dogarinsa ya gudu daga cikin motar
  • Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun kira iyalinsa kuma sun bukaci kudin fansa milyan hamsin

Etsako - Babban jami'n da sanda kuma DPO na ofishin Fugar dake jihar Edo, CSP Ibrahim Aliyu Ishaq, yayi arangama da tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Edo.

PRNigeria ta ruwaito cewa yan bindigan sun yi awon gaba da shi ne kusa Rafin Ise dake tsohuwar hanyar Auchi-Ekperi-Agenebode ranar Juma'a.

Rahoton ya kara da cewa tuni sun tuntubi iyalansa kan maganar kudin fansansa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake DPO na yan sandan da aka sace bayan kwanaki 6 hannunsu

Gabanin komarwa Edo, CSO Ishaq yayi DPO a ofishin yan sandan Dakata a jihar Kano.

A riwayar Solacebase, yan bindiga sun bukaci kudi N50m kafin su sake shi.

Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da DPO na yan sanda
Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da DPO na yan sanda
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel