'Yan majalisa sun nuna damuwa, sun bukaci sojoji da 'yan sanda su dakile hare-hare a hanyar Kaduna-Abuja
- 'Yan majalisar wakilai sun bukaci sojoji da 'yan sanda su dakile hare-hare a hanyar Kaduna zuwa Abuj
- Sun bayyana cewa yawan hare-haren da aka kai yankin a baya-bayan nan ya haifar da tsoro a zukatan al’umma da matafiya da ke bin hanyar
- Don haka majalisar ta bukaci Shugaban hafsan soji, Faruk Yahaya da sufeto janar na ‘yan sanda, Alkali Baba da su dauki matakin gaggawa kan lamarin
Majalisar wakilai ta bukaci Shugaban hafsan soji, Faruk Yahaya da sufeto janar na ‘yan sanda, Alkali Baba da su dauki matakin gaggawa don kakkabe hare-hare a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Majalisar ta yanke shawarar ne a ranar Laraba bayan ta aiwatar da wani kudirin gaggawa da Abubakar Nalaraba, dan majalisa daga jihar Nasarawa ya dauki nauyi.
A kwanan nan ne ‘yan bindiga suka kai hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna inda suka yi garkuwa da mutane da dama tare da kashe wasu.
A ranar Lahadi ne ‘yan bindiga suka kashe Sagir Hamida, wani dan takarar gwamna na jihar Zamfara a zaben 2019 a hanyar. Hakazalika sun yi garkuwa da wasu matafiya a yayin harin.
Da yake jagorantar muhawara kan lamarin, Nalaraba ya ce yawan hare-hare ya haifar da tsoro a zukatan al’umma da matafiya da ke bin hanyar, rahoton The Cable.
Ya ce:
“Muna sane da halin rashin tsaro da ake ciki yanzu a kasar nan kuma muna sane da yadda ake kashe yan Najeriya da dama sakamakon wadannan harr-hare.
“Yanzu bamu tsira ba a kasar nan. Hanyar Abuja zuwa Kaduna yan kasance daya daga cikin hanyoyi mafi yawan zirga-zirga musamman a karshen mako.
“Zai baka mamaki jin cewa hatta ya shugabannin hukumomin tsaro, manyan Jami’an tsaro, Janarori ba za su iya bin hanyar Abuja zuwa Kaduna ba tare da masu take masu baya da manyan sojoji ba, balle a kai ga maganar ‘yan Najeriya.”
Da yake bayar da gudunmawa ga kudirin, Ossai Ossai, daga jihar Delta, ya ce ya an tura kudade masu yawa ga tsaro amma babu wani ci gaba da aka samu, Tribune ta rahoto
‘Yan majalisar sun ce kasar na iya fuskantar wani rikici na abinci saboda babu tsaro a hanyoyi don zaryar kayan gona.
Bayan harin Lahadi, yan bindiga sun sake sace mutane ranar Litinin a titin Kaduna/Abuja
A baya mun kawo cewa tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da dimbin matafiya karo na biyu a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Lahadi, 22 ga Nuwamba, 2021.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa yan bindigan sun farmaki matafiya ne misalin karfe 4:30 na yamma kuma suka budewa matafiyan wuta.
Masu idanuwan shaida sun bayyana cewa kusan waje daya aka tare matafiya ranar Litinin da Lahadi.
Asali: Legit.ng