Jerin sunayen alkalai 22 da CJN ya rantsar na babban birnin tarayya

Jerin sunayen alkalai 22 da CJN ya rantsar na babban birnin tarayya

 • Shugaban alkalan Najeriya, Mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad, ya rantsar da sabbin alkalan babbar kotun tarayya a Abuja guda 22
 • A yayin rantsar da su a kotun koli, babban alkalin ya yi kira ga alkalan da su kawar da kai tare da gujewa duk wani rudani ko abinda zai bata musu suna
 • Ya sanar da cewa kasar nan a halin yanzu alkalai nagari ta ke bukata kuma kada su yarda rantsuwar ta tashi a banza domin abun tambaya ce ga Ubangiji

Abuja - Babban alkalin Najeriya, CJN Ibrahim Tanko Muhammad, a ranar Talata ya rantsar da sabbin alkalan babban kotun tarayya ta Abuja har guda 22.

Tanko ya yi kira garesu da su guje wa duk abinda suka san zai bata musu suna, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Minista Pantami ya jero dalilai 5 da suke nuna Najeriya a shirye take a bangare kasuwanci

Jerin sunayen alkalai 22 da CJN ya rantsar na babban birnin tarayya
Jerin sunayen alkalai 22 da CJN ya rantsar na babban birnin tarayya. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Babban alkalin yayin rantsar da alkalan a kotun koli da ke Abuja, ya yi kira garesu da su runtse idanuwansu kan duk wani abu da zai rude su ko kuma abinda zai kange su daga kaiwa kololuwar aikinsu.

Ya ce: "Shari'a ba ta mai son kai bace, ba ta mai son tara abun duniya ba ne kuma ba ta marasa dabi'a tagari ba ne da za a iya ba shi kwanon abinci ya sauya komai ba".

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Tanko yace, sabbin rantsatsun alkalan sun shiga wata rayuwa ne ta alkawari tsakaninsu da Ubangiji da kuma Najeriya, kuma duk abinda suka yi mai kyau zai kasance cikin ayyukansu masu kyau.

Tanko ya ce takardar da kalaman rantsuwar dole ne su samu matsuguni a zukatansu kuma dole ne a yi amfani da su yadda ya dace wurin hukunci da adalci.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace dan uwan hadimin Jonathan da wasu mutum 8 a Kwara

Ya ce a halin yanzu kasar nan ta na bukatar masu shari'a ne wadanda ke da lissafi, gaskiya da kankan da kai.

Hukumar kula da shari'a ta kasa ce ta zabo alkalan a watan Afirilun 2020.

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, Sabbin alkalan da aka rantsar su ne:

 1. Madugu Mohammed Alhaji (Oyo)
 2. Agunloye Kayode (Ondo)
 3. Enenche Eleojo (Kogi)
 4. Aminu Mohammad Abdullahi (Kano)
 5. Nwecheonwu Chinyere Elewe (Rivers)
 6. Ibrahim Mohammed (Jigawa)
 7. Sadiya Mu’azu Mayana (Zamfara)
 8. Kanyip Rosemary Indinya (Taraba)
 9. Aliyu Yunusa Shafa (Nasarawa)
 10. Mohammed Zubairu (Kaduna)
 11. Oluyemisi I. Adelaja (Osun)
 12. Fatima Abubakar Aliyu (Gombe)
 13. Agashieze Cyprian Odinaka (Enugu
 14. Aliyu Halilu Ahmed (Adamawa)
 15. Hafsat Lawan Abba-Aliyu (Yobe)
 16. Olufolake Olufolashade Oshin (Ogun)
 17. Nwabulu Ngozika Chineze (Anambra)
 18. Mimi Anne Katsina Alu-Apena (Benue)
 19. Binta Dogonyaro (Jigawa)
 20. Muhammad Mustapha Adamu (Kebbi)
 21. Jadesola Oludare Adeyemi-Ajayi (Ogun)
 22. Njideka Nwosu-Iheme (Rivers)

Asali: Legit.ng

Online view pixel