Ka cancanta: Jami'ar Afe Babalola ta karrama Zulum da digirin digirgir

Ka cancanta: Jami'ar Afe Babalola ta karrama Zulum da digirin digirgir

  • Jami’ar Afe Babalola da ke Ado Ekiti, jihar Ekiti ta karrama Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum
  • Jami'ar ta karrama Zulum ne da digirin digirgir a ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamba, saboda kokarin da yake yi wa jiharsa da al'umma
  • Gwamnan ya samu rakiyar manyan jami'an gwamnatin jihar Borno zuwa wajen karramawar

Jihar Ekiti - Jami’ar Afe Babalola da ke Ado Ekiti, jihar Ekiti ta karrama Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamba.

Jami’ar ta ce an karrama Zulum ne saboda namijin kokarin da yake yi tun bayan da ya zama gwamna a 2019.

Ka cancanta: Jami'ar Afe Babalola ta karrama Zulum da digirin digirgir
Ka cancanta: Jami'ar Afe Babalola ta karrama Zulum da digirin digirgir Hoto: The Governor of Borno State
Asali: Facebook

Shafin gwamnatin jihar Borno ya wallafa a Facebook cewa karrama gwamnan ne a yayin bikin yaye dalibai na jami’ar a karo na tara wanda gwamnan ya halarta a Ado-Ekiti.

Kara karanta wannan

2023: Na fasa tsayawa takarar shugaban kasa, Jigon PDP ya yi amai ya lashe bayan nema sau 3

Gwamna Kayode Fayemi ma ya halarci bikin yaye daliban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Uban jami’ar, Afe Babalola SAN, ya jinjinawa jajircewar gwamnan da sadaukarwarsa wajen yi wa mutanensa hidima.

Ya ce, karramawar ta duba karfin gwiwar Zulum, da kuma gaskiyarsa ta fuskar magance matsalolin da jiharsa ke fuskanta.

Shugaban jami’ar, Farfesa Smaranda Olarinde ya bayyana a wani taron manema labarai a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba cewa za a karrama Zulum saboda mutuncinsa da gudunmawarsa wajen ci gaban al’umma.

Gwamna Zulum ya samu rakiyar Sanata Abubakar Kyari na Borno ta arewa, Sanata Ali Ndume na Borno ta kudu, dan majalisar wakilai na mazabar Gubio, Magumeri da Kaga, Hon. Usman Zannah, mataimakin kakakin majalisar jihar Borno, Injiniya Abdullahi Askira.

Sauran sune; shugaban ma’aikata, Farfesa Isa Hussaini Marte, kwamishinan ilimi, Dr Babagana Mallumbe Mustapha, da shugaban jami’ar Borno, Farfesa Kyari Sandabe.

Kara karanta wannan

Gwamna Matawalle ya sake bude kasuwanni, ya ce lamarin tsaro ya inganta a Zamfara

'Yan gudun hijira na bukatar gidaje yayin da gwamnati za ta rufe sansanoninsu a Borno

A wani labarin, mun kawo a baya cewa da yawa daga cikin 'yan gudun hijaran da ke sansanin Bakasssi sun bayyana son komawarsu gida tare da komawa ayyukan nomansu domin samun rufin asiri a maimakon dogaro da tallafi.

Sai dai, sun bayyana damuwarsu kan makomar 'ya'yansu wadanda ke karatu a makarantun gaba da sakandare ba tare da wurin kwana ba, Daily Trust ta wallafa.

Gwamnatin jihar Borno a cikin kwanakin nan ta bayyana shirin ta na rufe dukkan sansanonin 'yan gudun hijira bayan dawowar zaman lafiya a yankunan da 'yan Boko Haram suke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel