Hotunan Zulum a sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi, ya bai wa masu komawa gida N.5b
- Babagana Umara Zulum gwamnan jihar Borno ya gwangwaje fiye da ‘yan gudun hijira 5000 da rabin biliyan
- Sun bayyana bukatar komawa garuwansu don ci gaba da rayuwa hakan ya sa gwamnan ya tallafa musu da makudan kudaden
- Zulum ya isa sansanin ‘yan gudun hijiran gwamnatin wanda aka fi sani da Bakassi a Maiduguri da misalin karfe 5:45am
Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya gwangwaje ‘yan gudun hijira fiye da mutane 5000 da rabin biliyan daya, Daily Trust ta ruwaito.
‘Yan gudun hijiran sun nuna bukatar komawa gidajensu ne don su cigaba da rayuwa. Gwamnan ya isa sansanin ‘yan gudun hijiran da misalin 5:45am inda aka fi sani da Bakassi a Maiduguri.
A takardar wacce hadimin gwamna Zulum ya saki, ya ce gwamnan ya yi sa’o’i 7 ya na jagorantar raba kudade da kayan abinci yayin da ya kai ziyarar ta ba-zata don tallafa wa mabukata da marasa gida saboda wasu mutanen su na zuwa sansanin ‘yan gudun hijiran tun safe sai dare su ke komawa gidajensu da sunan su ‘yan gudun hijira ne.
Sansanin na Bakassi, wanda gini ne da gwamnati ba ta kammala ginawa ba a kan titin Maduguri zuwa Damboa, cike ya ke da ‘yan gudun hijira da suka kai shekaru 7 a cikinsu.
Akwai ‘yan Monguno, Gwoza, Guzamala da karamar hukumar Marte. Mata da dama suna ta haihuwar yara kusan duk shekara.
Zulum ya nuna rashin amincewarsa da yadda sansanin ya zama wuri na dindindin da wasu suke yada zango ba tare da dagewa wurin taimakon kansu da kansu ba.
A cikin N500,000,000 din da gwamnan ya bayar yayin ziyarar ta sa, kowanne mace da namiji wadanda yawanci zawarawa ne sun samu N100,000, buhunan shinkafa 2 masu 25kg, katan na taliya da lita 5 na man girki.
Matan aure kuma sun samu N50,000 baya ga N100,000 da aka ba mazajensu tare da tarin kayan abincin.
'Yan bindiga a Katsina sun koma sadarwa tsakaninsu da waya mai amfani da mitar rediyo ta Walkie Talkie
Mata da dama da ke sansanin sun rasa mazajensu sakamakon fitinar ‘yan Boko Haram da ke halaka su, akwai wadanda kuma bata su ka yi, Daily Trust ta ruwaito.
“Da daman mazauna sansanin su na burin komawa gidajensu. Na zo nan ne don in taimaka musu su koma gidajensu. Mun zo da kayan abinci da kudade don su tallafa musu su fara rayuwa mai kyau idan sun koma”, a cewar Zulum.
Hadimin gwamnan ya ce, yayin da gwamnatin jihar Borno ta raba wa ‘yan sansanin gudun hijara N500,000,000 ta NED, sun kuma samar da kayan abinci don taimaka musu.
Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya samar da ma’aikatar jin kai da kuma NEDC don tallafa wa mutanen Borno da ke mawuyacin hali.
'Yan gudun hijira na bukatar gidaje yayin da gwamnati za ta rufe sansanoninsu a Borno
A wani labari na daban, da yawa daga cikin 'yan gudun hijaran da ke sansanin Bakasssi sun bayyana son komawarsu gida tare da komawa ayyukan nomansu domin samun rufin asiri a maimakon dogaro da tallafi.
Sai dai, sun bayyana damuwarsu kan makomar 'ya'yansu wadanda ke karatu a makarantun gaba da sakandare ba tare da wurin kwana ba, Daily Trust ta wallafa.
Gwamnatin jihar Borno a cikin kwanakin nan ta bayyana shirin ta na rufe dukkan sansanonin 'yan gudun hijira bayan dawowar zaman lafiya a yankunan da 'yan Boko Haram suke.
Asali: Legit.ng