Gwamnatin nan ba ta san hanyar magance halin da kasa ke ciki ba – Soyinka ya kawo shawara

Gwamnatin nan ba ta san hanyar magance halin da kasa ke ciki ba – Soyinka ya kawo shawara

  • Farfesa Wole Soyinka yace Najeriya tana neman ta wargaje, ana ji-ana gani, an gagara yin komai.
  • Shahararren marubucin ya bayyana wannan a wajen wani taro da aka shirya kwanan nan a Legas.
  • Soyinka ya na ganin gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta ma fahimci yanayin matsalolin kasar ba.

Lagos - Fitaccen marubucin Duniya, Farfesa Wole Soyinka yace Najeriya ta kama hanyar rugurgujewa, sannan gwamnati mai-ci ba ta da lakanin gyara.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Wole Soyinka yana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta da wata dabarar ceto kasar nan daga mawuyacin halin da ake ciki.

Farfesa Soyinka ya yi wannan magana a Freedom Park, jihar Legas yayin da yake tattaunawa kan takunkumin da aka kakabawa matafiya saboda cutar COVID-19.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya zata karbi bashin N290bn don samarwa yan Najeriya ruwan sha

An yi wa taron da aka yi a Legas take da: “COVID-19, fasaha da fatattakar mutanen gari.”

“Matsalar ita ce gwamnatin nan ba ta fahimci matsalolin da ke Najeriya ba. Idan muna jiran gwanatin nan ta kawo mafita, to muna cikin rudu.”
“Muna cikin wani irin mummunan yanayi. Kasar nan na cikin wani hali. Tana sukurkucewa a gaban idanmu. Gwamnatin nan ta rude.” - Soyinka.
Soyinka
Farfesa Wole Soyinka Hoto: dailypost.ng
Asali: Facebook

Guardian tace Farfesan ya kawo wannan magana ne yayin da aka yi masa tambaya game da shirin zaben gwamnan Anambra da ake sa rai za ayi a Nuwamba.

Mecece mafita a wurin Wole Soyinka?

Soyinka ya fadawa gwamnatin Najeriya cewa kuci-kucin dabarun da ta dauko na shawo kan matsalolin kasar nan ba za su taba yin aiki a halin da ake ciki ba.

Kara karanta wannan

A karon farko, an samu kungiyar da ta yi gagarumin biki domin bunkasa harshen Hausa

A cewar Soyinka, yadda za a shawo kan matsalolin da suka yi katutu shi ne a kira taron kasa, ta yadda kowace kabila za ta samu wakili da zai bada shawararsa.

Rahoton yace marubucin ya bada labarin wahalar da ya sha a hannun jami’an Najeriya a lokacin da zai yi tafiya zuwa kasar Faransa, yace lamarinsu babu tsari.

Ana fama da COVID-19, Dattijon mai shekaru 87 ya yi wata tafiya zuwa Faris da bai ji dadinta ba.

Farfesa Wole Soyinka yace Najeriya tana neman ta wargaje, ana ji-ana gani, an gagara yin komai. Shahararren marubucin ya bayyana wannan a makon nan.

Dr. Uchechi Iweala ya bar tarihi

Kwanan nan ne aka ji yaron Ngozi Okonjo-Iweala, Dakta Uchechi Iweala ya yi wa wani Bawan Allah aiki a gadon bayansa a asibitin Maryaland, kasar Amurka.

Uchechi Iweala kwararren Likita da ake ji da shi yanzu a Duniya. Iweala ya yi karatun likitanci a Harvard da wasu Jami’o’i a biranen New York da Washington DC

Kara karanta wannan

2023: Kungiyar Yarbawa ta tsaida ‘Dan takararta tilo a zaben Shugaban kasa daga APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel