Dakarun sojojin Nigeria sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram 38 cikin makonni 2, DHQ

Dakarun sojojin Nigeria sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram 38 cikin makonni 2, DHQ

  • Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce rundunar Operation Hadin Kai ta samu nasarar halaka a kalla ‘yan Boko Haram 38 cikin makonni 2
  • Mukaddashin darekta janar na watsa labaran soji, Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan yayin sanar da nasarorin sojin
  • Ya bayyana yadda su ka kama ‘yan ta’adda 11 har da masu ba su bayanan sirri da kayan abinci sannan su ka ceto wasu da aka sace

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ce rundunar Operation Hadin Kai ta sojojin Nigeria ta samu nasarar halaka a kalla ‘yan Boko Haram 38 a cikin makonni 2 cikin sanarwar da ta fitar a shafinta na Facebook.

Bernard Onyeuko, mukaddashin darektan watsa labaran soji ya sanar da hakan yayin bayar da bayani akan ayyukan da sojoji su ka aiwatar tsakanin ranar 14 ga watan Oktoba zuwa 28 ga watan.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun mamaye gidan rasuwa, sun sace bakin da suka halarci jana’iza

Dakarun sojojin Nigeria sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram 38 cikin makonni 2, DHQ
Bernard Onyeuko, mukadashin watsa labarai na sojojin Nigeria. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Onyeuko ya ce an kama ‘yan ta’adda 11 tare da masu kai mu su labarai da kuma masu kai mu su bayanan sirri har da ma su kai mu su kayan masarufi kamar yadda ya zo cikin sanarwar.

Har ila yau, ya ce su na tsaka da ayyukan su su ka samu nasarar ceto wasu da aka yi garkuwa da su.

Ya ce rundunar ta kwato makamai 29, bindigogi masu jigida guda 2, jakunkunan taki 622 da su ke amfani da su wurin hada abubuwa ma su fashewa da sauran su.

Onyeuko ya kara da bayyana yadda su ka ci nasarorin a kauyaku kamar Dar, Kumshe, Wulgo, Chanbol da Kijmatari da ke jihar Borno.

Sannan har wuraren Ngela zuwa Wulgo da Nguru zuwa titinan Kano ma sun halaka ‘yan ta’addan. Har kauyakun Dikwa, Mafa da Ngama da ke jihar Yobe ma ba a bar su a baya ba.

Kara karanta wannan

Bayan shekara 1, Rundunar soji ta ki mayar da Kanal din da ya halaka 'yan Boko Haram 377 bakin aikinsa

Da yawa sun zubar da makaman su

Onyeuko ya ce ‘yan ta’adda 1,999 da ‘yan uwan su ciki akwai maza 114, mata 312 da yara 773 duk sun zubar da makaman su a yankuna daban-daban na arewa maso gabas.

Sojin sama sun yi wa ‘yan Boko Haram ragargaza ta sama wuraren Malam Fatori da yankin tafkin Chadi.

Ya ce an samu duk wadannan bayanan ne daga majiya mai karfi ta sirri da ke yankin.

Ya kara da cewa:

“Sakamakon harbe-harben da sojojin sama su ka yi, sun ragargaji jirgin ruwan ‘yan ta’adda wanda ya yi sanadin halaka su da kuma ji ma wasu ciwuka da dama.”
“Sannan a ranar 21 ga watan Oktoba, sojin sama sun yi harbe-harbe a jihar Yobe inda su ka halaka ‘yan ta’adda da dama.”

Rahoto: Masu ƙera wa Boko Haram bama-bamai sun koma dazukan Kudancin Kaduna

A jiya, kun ji cewa shugabannin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga Bakoura Buduma sun mayar da masu hada musu bama-bamai dazukan yankin kudanci Kaduna, a cewar wani rahoton da PRNigeria ta fitar.

Kara karanta wannan

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

A baya-bayan nan ne aka mayar da masu hada bama-baman da ake kira Amaliyyah a tsakin 'yan ta'addan, zuwa Rijana, Igabi da Chikun a yankin kudancin Kaduna.

Majiyoyi daga ciki sun ce kungiyoyin biyu na Boko Haram za su yi amfani da duwatsun da ke yankin a matsayin mabuya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel