NAFDAC ta garkame wasu kamfanoni 27 na 'Pure Water' saboda rashin inganci da tsafta
- Hukumar NAFDAC ta rufe wasu kamfanonin da ke samar da ruwan leda mara inganci a wasu sassan Najeriya
- Hukumar ta bayyana cewa, ta dukufa wajen tabbatar da an samar da ruwa mai tsafta da inganci ga 'yan Najeriya
- Kungiyar masu samar da ruwan leda sun bayyana irin kalubalen da suke fuskanta a sana'ar ta su ta samar da ruwa
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta ce, duk wani ruwan ledan da bai da lambar NAFDAC, da kyakkyawan rubutu hade da mummunan nahawu wajen rubutu to a sani ruwan bogi ne kuma mara tsafta.
Darakta-Janar na NAFDAC, Mojisola Adeyeye, ta ce tuni hukumar ta rufe kamfanin ruwa guda 27 saboda sun ki bin ka’idojin samar da ruwa mai inganci, inji rahoton BBC Pidgin.
Ta bayyana hakan ne a yayin taron kungiyar masu samar da ruwan leda ta kasa ta Najeriya.
Ta bayyana cewa hukumar ta dauki matakin ne don tabbatar da cewa ana kula da tsaftar masana'antar ruwan da ake samarwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Misis Adeyeye ta ce tsakanin watan Janairu zuwa Agusta 2021, an rufe masana'antun ruwa 27.
Ta kara da cewa dole ne su bi tsarin masana'antu kafin su bude kamfanonin don ci gaba da aiki a nan gaba.
Masana'antar ruwa
Misis Adeyeye ta ce sana’ar samar da ruwan leda sana’a ce ta biliyoyin nairori, shi ya sa hukumar ta dauki lamarin da muhimmanci.
A cewarta:
“Baya ga fa’idar tattalin arziki, alfanun kiwon lafiya suna da yawa kuma idan kun daidaita, da kun sami riba mai yawa ta gudummawar NAFDAC don tabbatar da tsarin ci gaban kiwon lafiya gaba daya.
"Wannan shine dalilin da ya sa NAFDAC ta tabbatar da cewa akwai cikakkiyar himma ga batun inganci da daidaito."
Ta kuma ce hukumar ta NAFDAC ta yi wa sabbin masana’antun ruwa 2,153 rajista a kasar tsakanin watan Janairu zuwa Agusta, 2021.
Masu samar da ruwan leda ba bisa ka'ida ba
A nata jawabin, shugabar ATWAP ta kasa, Clementina Ativie, ta ce masu samar da ruwan bogi da kuma masu sana’ar ba bisa ka’ida ba na daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar harkar ruwa.
Ta yi nuni da cewa rashin samun wutar lantarki a wasu yankunan kasar ma na daga kalubale ga harkar.
Premium Times ta ruwaito ta tana cewa:
“Rashin wutar lantarki; ya sa mu dogara da injinan dizal tare da karin farashi kan samarwar, haraji da yawa da ayyukan da hukumomin gwamnati ke yi a kowane mataki."
Ta ce duk da wadannan kalubalen, masana'antar har yanzu tana kokarin baiwa al'ummar Najeriya kyakkyawan sakamako.
Ms Ativie ta bayyana cewa mambobin ATWAP sun haura mutane 16,000 a fadin kasar.
Ta ce kowane mamba yana daukar ma’aikata kusan mutane 15 kai tsaye da kuma karin mutane kusan 15 a fakaice.
Ta kara da cewa:
"Saboda haka muna daukar ma'aikata kusan mutane miliyan daya da dubu dari shida a harkar samar da ruwan leda, wanda ya hada da masu rarrabawa, dillanci da sarrafa shara."
Burodi ya zama nama: Tsadar burudo da 'Pure water' ya addabi babban birni Abuja
A bangare guda, mazauna a Abuja da wasu sassan yankunan jihar Neja sun shiga damuwa kan sabon farashin burodi da ruwan leda na 'pure water' da ya soma a karshen watan jiya da makon farko na watan Oktoba.
Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya fitar da rahoton cewa karuwar farashin ta faru duk da cewa wasu abubuwan basu da alaka da rashin tsaro, tsadar kayan masarufi da canjin Naira zuwa dala.
Jakar ruwan 'pure water' da a da ake siyarwa a farashin N100 yanzu ya cilla zuwa tsakanin N200 zuwa N250, yayin da ake siyar da guda akan N20 sabanin N10 a watannin baya, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng