Burodi ya zama nama: Tsadar burudo da 'Pure water' ya addabi babban birni Abuja

Burodi ya zama nama: Tsadar burudo da 'Pure water' ya addabi babban birni Abuja

  • An fara kokawa kan hauhawar farashin burudi da ruwan pure water a babban birnin tarayya
  • Wannan na zuwa ne yayin da kamfanoni suka kara farashin kayayyakinsu da yawa a yankin
  • Kungiyoyi sun bayyana dalilai da yawa da suka jawo irin wadannan sauye-sauyen farashi

Abuja - Mazauna a Abuja da wasu sassan yankunan jihar Neja sun shiga damuwa kan sabon farashin burodi da ruwan leda na 'pure water' da ya soma a karshen watan jiya da makon farko na watan Oktoba.

Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya fitar da rahoton cewa karuwar farashin ta faru duk da cewa wasu abubuwan basu da alaka da rashin tsaro, tsadar kayan masarufi da canjin Naira zuwa dala.

Jakar ruwan 'pure water' da a da ake siyarwa a farashin N100 yanzu ya cilla zuwa tsakanin N200 zuwa N250, yayin da ake siyar da guda akan N20 sabanin N10 a watannin baya, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Gwamnatin Neja ta ce za ta sa kafar wando daya da masu ba 'yan bindiga bayanai

Burodi ya zama nama: 'Yan Abuja sun shiga wani hali sakamakon tsadar burodi da 'Pure water'
Ruwan Leda | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Dasuma Friday, wani mai buga ruwan 'pure water', da ya ke bayyana dalilan da ke haifar da tashin farashi, ya bayyana cewa wasu abubuwan da ke jawo hawan farashi sun hada da tsadar buga ledar da kuma kudin wutar lantarki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran, a cewarsa, sun hada da biyan haraji ga hukumomi biyu da kuma tsadar siyan man janareta.

Mista Friday ya bayyana cewa idan tsohon farashin ya ci gaba a yanzu, mai bugawa shi zai kwan ciki ya tafka asara, yana mai jaddada cewa gaskiyar tsadar kayan dole ya karu.

Kungiyar masu buga ruwa na leda ta fara yajin aiki da nufin fahimtar da jama'a cewa kasuwancin ba zai dore ba sai sun yarda da canjin farashin.

Bangaren masu burodi

An kuma ruwaito cewa farashin burodi ya kuma shafi sabon hauhawar farashi.

Burodi da aka sayar a baya N500 yanzu ana siyar da shi N700 yayin da wanda ake siyarwa N200 yanzu ke tafiya akan N300.

Kara karanta wannan

Matashi ya maka IGP, DG na DSS da wasu manya a kotu kan cin zarafin 'yan Shi'a

Kungiyar Manyan Masu Burodi da Masu Abinci na Najeriya (AMBCN) reshen Abuja, ta bayyana dalilin karuwar, ta bayyana cewa tsadar kayan masarufin kwaba burodi ne ke da alhakin karin.

Ishaq Abdulkareem, Shugaban AMBCN, ya ce karin 30% cikin dari na kari kan farashin burodi an yi shi ne don gujewa rufe gidajen burodi da tsadar kayan masarufi ya shafa.

Mista Abdulkareem ya bayyana cewa farashin duk abubuwan da ake amfani da su don yin burodi sun tashi, musamman fulawa da sukari.

Ya bayyana cewa kudin yin rijistar kasuwanci yana cikin dalilai, ya kara da cewa kafin yanzu, kudin yin rijistar ya kai N32,500 amma a yau ya kai N90,000.

Maria Cardillo, Babbar Darakta ta Bon Bread, ta ce akwai bukatar a kara farashin burodi don gujewa durkushewar kasuwanci.

Ta bayyana cewa ana bukatar a kara farashin burodi saboda "mun sami hauhawar farashin albarkatun kasa kuma ba mu da wasu hanyoyin."

Kara karanta wannan

Na fi zama cikin nishadi da farin ciki yayin da nake cikin fatara, Mawaki Akon

Bangarori da yawa sun bayyana abubuwan da ke jawo tashe-tashen farashin kayayyaki a kasar.

A bangare guda Vanguard ta rahoto wani dan majalisa Mohammed Monguno, Babban Bulaliyar majalisar wakilai ya gabatar da kudirin dokar daidaita farashin abinci a kasar.

Dokar mai taken, "Dokar Canza Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, 1999 don yin tanadi na 'yancin Abinci da Tsaro a Najeriya".

Kudirin ya nemi tilastawa bangaren zartarwa na gwamnati da ya daidaita farashin abinci da sauran abubuwa, don tabbatar da wadatar abinci da rage wahalar tattalin arziki kan yawancin 'yan Najeriya.

Tsadar abinci: Dalilin da yasa 'yan Najeriya za su ci gaba da cin bakar wahala, in ji masana

A wani labarin, masana tattalin arziki a Najeriya na gargadin cewa zai yi matukar wuya a iya cimma hasashen nan da babban bankin kasar CBN ya yi na sa ran saukar farashin kayayyaki.

Babban bankin ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2022, farashin kayan abinci zai sauka da 10% cikin 100%, saboda mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da kuma rashin bin matakan da suka kamata.

Kara karanta wannan

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Kasimu Garba Kurfi, wani masanin tattalin arziki da ke birnin Legas, yana cikin masu irin wannan ra'ayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.