An kama wani matashi bayan ya yi barazanar sace Shugaban al’umman Hausawa a Benin

An kama wani matashi bayan ya yi barazanar sace Shugaban al’umman Hausawa a Benin

  • 'Yan sanda a jihar Edo sun kama wani matashi mai suna Yakubu Idris
  • Idris ya shiga hannu ne bayan ya yi barazanar sace shugaban Hausawa a garin Benin, Alhaji Badamasi Saleh
  • Saleh dai ya shigar da kara ofishin 'yan sanda bayan kira da ya samu daga matashin wanda bai san ko wanene ba, inda ya ce an biya shi don ya sace shi

Jihar Edo - Jami’an ‘yan sandan jihar Edo sun kama wani mazaunin Kano mai shekaru 21, Yakubu Idris.

An kama Idris ne bisa zargin cewa yana barazanar yin garkuwa da shugaban Hausawa a garin Benin, Alhaji Badamasi Saleh, jaridar Daily Trust ta rahoto.

An kama wani matashi bayan ya yi barazanar sace Shugaban al’umman Hausawa a Benin
An kama wani matashi bayan ya yi barazanar sace Shugaban al’umman Hausawa a Benin Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wanda ake zargin ya shiga hannu ne bayan korafi da Alhaji Badamasi Saleh ya shigar kan cewa wani mutum da bai san ko wanene ba yana barazanar sace shi.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun hari ofishin 'yan sanda, sun kashe 3, an hallaka dan bindiga 1

An tattaro cewa a ranar 16 ga watan Satumba, Saleh ya rubuta kara ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Edo cewa wani mutum da bai san ko wanene ba wanda ya yi ikirarin cewa shi dan kungiyar masu garkuwa da mutane da ke Birnin-Gwari, jihar Kaduna ne, ya yi barazanar sace shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanda ake zargin ya fada ma Saleh cewa wani na kusa da shi ya biya sa naira miliyan 1 domin ya sace shi amma ya yanke shawarar sanar da shi shirin saboda shi mutumin kirki ne, rahoton PM News.

Wanda ake zargin ya ce lallai sai Saleh ya biya naira miliyan 1 zuwa asusun banki domin hana mambobin kungiyarsa aiwatar da shirin sace shi din.

An tattaro cewa ‘yan sanda sun nemi Saleh ya yi yadda mutumin ya nema sannan ya tattauna da shi inda aka kama shi bayan an biya kudin a cikin asusun bankin da ya bayar.

Kara karanta wannan

Tsananin kishi ya sa saurayi ture budurwarsa har lahira a Bauchi

Da aka tuntube shi, kakakin ‘yan sandan jihar, Kontongs Bello, ya tabbatar da kamun nasa.

Ya ce an bukaci mai karar ya tattauna da wanda ake zargin inda ya yarda a biya N100,000, an kuma biya kudin a asusun da ya bayar.

Ya ce da suka samu labarin cewa an biya kudin a cikin asusun, sai ‘yan sanda suka kama wanda ake zargin a mafakarsa da ke jihar Kano.

Kontongs ya kara da cewa a yayin bincike, an gano cewa wanda ake zargin ya kasance wani da mai karar ya taba taimakawa a baya yayin da yake a Benin.

An kuma kai hari: Miyagun yan bindiga sun hallaka mutum 6, sun sace wasu dama a jihar Katsina

A wani labarin, miyagun yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 6, sun yi awon gaba da wasu a wani sabon hari da suka kai jihar Katsina.

Jaridar Premium Times tace maharan sun kai harin ne ƙauyen Unguwar Samanja dake ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Na shirya siyar da kaina - In ji wani matashi da talauci ya ishe shi a Kano

Jihar Katsina dai, itace jihar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya fito kuma tana fama da hare-haren yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng