Zainab Ahmed: FG za ta dena biyan tallafin man fetur bayan wata 6 na farkon 2022

Zainab Ahmed: FG za ta dena biyan tallafin man fetur bayan wata 6 na farkon 2022

  • Ministan kudi Zainab Ahmed ta ce gwamnatin Nigeria za ta dena biyan tallafin man fetur a watanni 6 na karshen 2022
  • Ministan ta bayyana hakan ne wurin taron tattalin arziki na Nigeria karo na 27 da aka yi a ranar Litinin a Abuja
  • Doyin Salami, shugaban kwamitin bada shawarwari na tattalin arziki, EAC, ya ce dama biyan tallafin saba sabuwar dokar man fetur na PIA

Abuja - The Cable ta rahoto cewa Zainab Ahmed, ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare, ta ce gwamnatin tarayya za ta biya tallafin man fetur na watanni shida na farkon shekarar 2022.

Ta bayyana hakan ne a ranar Litinin wurin taron tattalin arziki na Nigeria karo na 27 (NES#27) a Abuja.

Kara karanta wannan

Mai zai iya kara tsada, Gwamnati za ta daina biyan tallafin fetur a tsakiyar shekara mai zuwa

Zainab Ahmed: FG za ta dena biyan tallafin man fetur bayan wata shida na farkon 2022
Ministan Kudi da Kasafin Kudi, Zainab Ahmed. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Ahmed ta ce daga watan Yulin 2022, gwamnati za ta janye hannun ta daga bangaren man fetur da iskar gas kamar yadda ya zo a ruwayar ta The Cable.

A cikin watanni bakwai, an kashe biliyan 714 don biyan tallafin man fetur, hakan na rage adadin kudaden da gwamnatin tarayya ke samu duk wata.

A halin yanzu, kamfanin man fetur ta Nigeria, NNPC, ita ce kadai ke shigo da man fetur kasar, kuma tana cire kudin tallafin man fetur daga matakai uku na gwamnati tunda ba a yi tanadin hakan ba a kasafin kudin 2021.

Ahmad ta ce:

"A kasafin kudin mu na 2022, wata shidan farko na shekara za mu biya tallafin man fetur; muna shirin janye dukkan tallafi a wata shida na karshen shekara, za mu samu karin kudin shiga daga bangaren man fetur da gas da kuma kasashen waje."

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Buhari zai ba masu digiri bashin miliyoyi saboda rage zaman banza

Ya kamata a janye tallafin man fetur baki daya, Salami

A jawabinsa wurin taron, Doyin Salami, shugaban kwamitin bada shawarwari na tattalin arziki, EAC, ya ce ya dade yana bada shawarar a janye tallafin man fetur baki daya.

Ya ce sabon dokar man fetur na PIA, ya haramta biyan tallafin man fetur. Don haka bin doka shine abin da ya dace kuma hakan zai haifar da alheri da cigaba ga kasa.

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje

A wani labarin, kun ji cewa bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.

Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.

Kara karanta wannan

Sai mun hada kai ne za mu iya cin galaba a kan miyagu – APC kan harin jirgin kasa

Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel