Buhari ya yi wa tsoffin sojojin Biyafara 102 afuwa, ya amince da biyansu kudin sallama

Buhari ya yi wa tsoffin sojojin Biyafara 102 afuwa, ya amince da biyansu kudin sallama

  • Fadar shugaban kasa ta yi afuwa ga tsoffin sojojin da suka yi fafutukar Biyafara a lokacin yakin basasa
  • Ministan tsaro, Bashir Magashi, a ranar Juma’a, 15 ga watan Oktoba, ya sanar da cewar za a kuma biya tsoffin sojin kudin sallama
  • Wannan labarin mai dadi na zuwa ne shekaru 51 bayan mummunan lamarin wanda ya hadd sa kashe-kashe da radadi a kasar

Hukumar fansho ta sojoji ta yi wa tsoffin sojojin Biyafara kimanin su 102 rijista domin biyansu kudin sallama da sauran hakoki.

Ministan taro, Bashir Magashi wanda ya sanar da hakan, ya kuma bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa tsoffin sojin na Biyafara afuwa, PM News ta rahoto.

Buhari ya yi wa tsoffin sojojin Biyafara 102 afuwa, ya amince da biyansu kudin sallama
Buhari ya yi wa tsoffin sojojin Biyafara 102 afuwa, ya amince da biyansu kudin sallama Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Magashi ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 15 ga watan Oktoba, yayin bikin tunawa da ranar joji na 2022 a Abuja, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

Kalamansa:

“Za ku yi farin ciki da sanin cewa Hukumar Fansho ta Sojoji ta kammala tantance tsoffin sojojin Biyafara su 102 wadanda shugaban kasa ya yi wa afuwa.
“Yakin ya kare shekaru 51 da suka wuce kuma da dama daga cikin wadanda ke da hannu a lamarin basa raye amma wadanda ke da korafi na hakika suna iya fitowa da ikirarinsu domin dubawa.”

Ku biya ƴan kudu diyyar asarar da suka tafka lokacin yaƙin Biyafara, Gwamnan Kudu ya faɗawa gwamnatin Buhari

A wani labarin, Hope Uzodimma, gwamnan jihar Imo ya yi kira ga gwamnatin tarayya akan samar da kudade na musamman don biyan yankin kudu maso gabas asarorin da su ka tafka yayin yakin basasa.

Jaridar The Cable ta ruwaito Uzodimma ya yi wannan bayanin ne a Owerri, babban birnin jihar Imo a ranar Laraba yayin wani taro na tattaunawa akan hanyoyin rarraba kudaden harajin jihar wanda hukumar rarraba kudaden haraji (RMAFC) ta shirya.

Kara karanta wannan

Buhari ya ce gwamnatinsa ta shirya za ta fara kera makamai saboda wasu dalilai

Gwamnan ya ce idan aka samar da kudade na daban za su taimaka wurin biyan mutanen da su ka yi asarar dikiyoyin su da rayukan ‘yan uwan su yayin yakin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel