Ku biya ƴan kudu diyyar asarar da suka tafka lokacin yaƙin Biyafara, Gwamnan Kudu ya faɗawa gwamnatin Buhari

Ku biya ƴan kudu diyyar asarar da suka tafka lokacin yaƙin Biyafara, Gwamnan Kudu ya faɗawa gwamnatin Buhari

  • Hope Uzodinma, gwamnan jihar Imo ya yi kira ga gwamnatin tarayya akan tallafa wa dangane da asarorin da yakin basasa ya janyo aka tafka
  • A cewar sa, ya kamata gwamnatin tarayya ta samar da wasu kudi na musamman don biyan yankin kudu maso gabas asarorin da su ka tafka
  • Uzodimma ya yi wannan jawabin ne a Owerri, babban birnin jihar Imo a ranar Laraba a yayin wani taro wanda hukumar RMAFC ta shirya

Imo - Hope Uzodimma, gwamnan jihar Imo ya yi kira ga gwamnatin tarayya akan samar da kudade na musamman don biyan yankin kudu maso gabas asarorin da su ka tafka yayin yakin basasa.

Jaridar The Cable ta ruwaito Uzodimma ya yi wannan bayanin ne a Owerri, babban birnin jihar Imo a ranar Laraba yayin wani taro na tattaunawa akan hanyoyin rarraba kudaden harajin jihar wanda hukumar rarraba kudaden haraji (RMAFC) ta shirya.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Ku biya ƴan kudu diyyar asarar da suka tafka lokacin yaƙin basasa, Gwamnan Kudu ya faɗawa gwamnatin Buhari
Gwamna Hope Uzodinma da Shugaba Muhammadu Buhari. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya ce idan aka samar da kudade na daban za su taimaka wurin biyan mutanen da su ka yi asarar dikiyoyin su da rayukan ‘yan uwan su yayin yakin.

Kamar yadda ya ce:

“Ina kyautata zaton yakin basasan ne ya sanya yankin kudu maso gabas a matsananciyar fatara; an kone mu su gidajen su sannan an halaka rayuka.”
“Kwanan nan na ga aka samar da wata hukumar bunkasa arewa maso gabas, sakamakon asarorin da Boko Haram ta janyo. Amma watanni 30 da aka yi ana yakin basasa wacce ta kare a 1970 ta bar kudu maso gabas a cikin mawuyacin hali.”

A cewar Uzodimma, an taba duba wannan tsarin raba kudaden harajin ne a 1992.

Ya ce kudu maso gabas ta girgiza kwarai

Gwamnan ya ce kudu maso gabas ta sha bakar wahala saboda rashin adalcin da ake yi mata wurin raba kudaden harajin da ake samu daga yankin.

Kara karanta wannan

Sakin Nnamdi Kanu zai kawo ƙarshen rashin tsaro a kudu maso gabas, Sanata Ubah

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, Uzodimma ya kara da cewa:

“A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ta na tafiya da kaso 52.68%, jihohi su tafi da 26.72% yayin da kananun hukumomi 774 da ke Najeriya su ke tafiya da 2.60%."

Ya kara da bayyana yadda jihar Imo take da kamfanoni 7 da suke samar da man fetur amma cikin kuskure aka mika wa jihar Rivers rijiyoyin mai 43.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya akan samar da kamfanonin hada sinadarai da takin gona a kasa don samar wa matasa ayyukan yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel