Buhari ya yi wa tsoffin sojojin Biyafara 102 afuwa, ya amince da biyansu kudin sallama
- Fadar shugaban kasa ta yi afuwa ga tsoffin sojojin da suka yi fafutukar Biyafara a lokacin yakin basasa
- Ministan tsaro, Bashir Magashi, a ranar Juma’a, 15 ga watan Oktoba, ya sanar da cewar za a kuma biya tsoffin sojin kudin sallama
- Wannan labarin mai dadi na zuwa ne shekaru 51 bayan mummunan lamarin wanda ya hadd sa kashe-kashe da radadi a kasar
Hukumar fansho ta sojoji ta yi wa tsoffin sojojin Biyafara kimanin su 102 rijista domin biyansu kudin sallama da sauran hakoki.
Ministan taro, Bashir Magashi wanda ya sanar da hakan, ya kuma bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa tsoffin sojin na Biyafara afuwa, PM News ta rahoto.
Magashi ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 15 ga watan Oktoba, yayin bikin tunawa da ranar joji na 2022 a Abuja, kamar yadda Punch ta rahoto.
Kalamansa:
“Za ku yi farin ciki da sanin cewa Hukumar Fansho ta Sojoji ta kammala tantance tsoffin sojojin Biyafara su 102 wadanda shugaban kasa ya yi wa afuwa.
“Yakin ya kare shekaru 51 da suka wuce kuma da dama daga cikin wadanda ke da hannu a lamarin basa raye amma wadanda ke da korafi na hakika suna iya fitowa da ikirarinsu domin dubawa.”
Ku biya ƴan kudu diyyar asarar da suka tafka lokacin yaƙin Biyafara, Gwamnan Kudu ya faɗawa gwamnatin Buhari
A wani labarin, Hope Uzodimma, gwamnan jihar Imo ya yi kira ga gwamnatin tarayya akan samar da kudade na musamman don biyan yankin kudu maso gabas asarorin da su ka tafka yayin yakin basasa.
Jaridar The Cable ta ruwaito Uzodimma ya yi wannan bayanin ne a Owerri, babban birnin jihar Imo a ranar Laraba yayin wani taro na tattaunawa akan hanyoyin rarraba kudaden harajin jihar wanda hukumar rarraba kudaden haraji (RMAFC) ta shirya.
Gwamnan ya ce idan aka samar da kudade na daban za su taimaka wurin biyan mutanen da su ka yi asarar dikiyoyin su da rayukan ‘yan uwan su yayin yakin.
Asali: Legit.ng