Jerin jihohi 7 da ke rike da tarin albashin malaman makarantun Firamare

Jerin jihohi 7 da ke rike da tarin albashin malaman makarantun Firamare

Wasu adadi na gwamnatocin jihohi a Najeriya na rike tarin basussuka na albashin malaman firamare na gwamnati, alawus-alawus da kuma karin girmansu.

Mafi akasarin wadannan malamai sun koka kan yadda jihar ta ki biyan su albashi yadda ya kamata a kuma lokacin da ya dace sakamakon halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a yanzu.

Jerin jihohi 7 da ke rike da tarin albashin malaman makarantar Firamare
Jerin jihohi 7 da ke rike da tarin albashin malaman makarantar Firamare Hoto: Thomas Imo/Photothek
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa malaman na firamare na bin wasu gwamnatocin jihohi tarin albashi kama daga kimanin watanni 6 zuwa 15.

An tattaro cewa akwai tarin albashin da ba a biya ba daga shekarun baya kuma a matakai daban-daban na rukunin malamai daban-daban.

Koda dai babu wani dalili da jihohin suka bayar a matsayin abun da ya hana biyan malaman na firamare, wasu sun gano jiran kudi daga gwamnatin tarayya a matsayin makasudin jinkirin da ake samu wajen biyan albashin.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jihohin Najeriya da malaman firamare ke bi kudi

Ga jerin sunayen jihohin da ke rike da albashin malaman a bisa ga rahoton:

1. Kaduna

2. Neja

3. Benue

4. Taraba

5. Imo

6. Rivers

7. Ondo

Junairu 2022 za'a karawa Malaman makarantun Najeriya albashi, Ministan Ilimi

A wani labarin, mun kawo a baya cewa aramin Ministan ilimin Najeriya Emeka Nwajuiba, ya bayyana cewa za'a fara biyan Malaman Makarantu sabon albashin da Shugaba Buhari ya musu alkawari daga Junairun 2022.

Nwajiuba ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 30 ga Satumba a wani taro da ma'aikatar Ilimi ya shirya a Abuja, rahoton Premium Times.

An shirya taron ne don tarban ranar Malaman duniya da za'a yi ranar 5 ga Oktoba, 2021. Ministan wanda ya samu wakilcin Sakataren ma'aikatar, Sonnu Echono, ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

El-Rufa'i ya kafa majalisar tantance wa'azi da Malamai masu wa'azi a jihar Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel