Junairu 2022 za'a karawa Malaman makarantun Najeriya albashi, Ministan Ilimi
- Ministan Ilimi ya yiwa Malaman Najeriya Albishiri da karin albashi a sabon shekara
- A bara, Buhari yayi Malamai alkawarin yi musu karin albashi da lokacin ritaya
- Ya yi kira ga Gwamnoni su tabbatar da cewa suma sun yi hakan a jihohinsu
Abuja - Karamin Ministan ilimin Najeriya Emeka Nwajuiba, ya bayyana cewa za'a fara biyan Malaman Makarantu sabon albashin da Shugaba Buhari ya musu alkawari daga Junairun 2022.
Nwajiuba ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 30 ga Satumba a wani taro da ma'aikatar Ilimi ya shirya a Abuja, rahoton Premium Times.
An shirya taron ne don tarban ranar Malaman duniya da za'a yi ranar 5 ga Oktoba, 2021.
Ministan wanda ya samu wakilcin Sakataren ma'aikatar, Sonnu Echono, ya bayyana hakan.
Yace:
"Shugaban kasa ya amince da sabon tsarin albashi kuma zamu kammala nan ba da dadewa ba."
"Shugaban ya ce a fara wannan kari daga 2022."
"Muna kokarin kammalawa don ganin cewa Malaman zasu fara samun albashi da suka cancanta daga Junairun 2022."
Gwamnoni ya rage yanzu su dabbaka wannan tsari
Ministan ya ce yanzu abinda ya rage shine gwamnoni da yan majalisar dokokin tarayya suyi abinda ya dace wajen tabbatar da aiwatar da wannan kari.
Yace:
"Abinda ya rage yanzu shine sauran masu hakki irinsu gwamnoni, majalisar dokoki da sauransu su bada hadin kai wajen ganin cewa an aiwatar da wannan abu ba tare da matsala ba."
"Misali, mun gaji da maganganun cewa an ki biyan Malaman makarantu albashin watanni."
"Wannan babban laifi ne."
Ministan ya kara da cewa sauran abubuwan da za'a inganta Malamai da su sune gidaje da horar da su.
Hakazalika yace za'a kara shekarun aikinsu daga 35 zuwa 40.
Oct 1: Shugaba Buhari zai yi wa mutanen Najeriya jawabi na musamman ranar bikin samun ‘yanci
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari zai yi wa al’umma jawabi na musaman a safiyar ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoba, 2021.
Mai girma Muhammadu Buhari zai yi magana da karfe 7:00 na safe a matsayin ayyukan bikin ranar samun ‘yancin kai da Najeriya za tayi a shekarar nan.
Femi Adesina wanda yake magana da yawun bakin shugaban kasa, ya bayyana wannan dazu.
Asali: Legit.ng