Buhari, Natasha da Wasu Fitattun Ƴan Najeriya da Aka fi Karanta Labaransu a 2025

Buhari, Natasha da Wasu Fitattun Ƴan Najeriya da Aka fi Karanta Labaransu a 2025

  • Sanata Natasha Akpoti ce ta fi shahara a duniya a cikin abubuwan da yan Najeriya suka fi nema a kafar bincike ta Google a shekarar nan
  • Rahoton da Google ya fitar na 2025 ya nuna yadda 'yan Najeriya suka rika bincike kan siyasa, rikice-rikicen duniya, mutuwa da nishadi
  • A 2025, mutane sun yi bincike sosai kan rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, an yi duba kan tarihin mulki da tasirinsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin Google ya fitar da rahoton binciken shekarar 2025, inda ya bayyana cewa Sanata Natasha Akpoti daga Kogi ta zama wacce aka fi binciken labaranta a Najeriya.

Kamfanin ya ce sanatar ta ja hankalin jama’a sosai yayin da al’umma ke bibiyar rikicinta da Sanata Godswill Akpabio da tasirin siyasarta da kuma rikice-rikicen da suka kewaye zabukan Kogi.

Kara karanta wannan

Badaru ya ƙaryata jita jitar da ake yaɗawa game da murabus daga kujerarsa

Google ta fitar da bayanan mutane da aka fi karanta labaransu a 2025
Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari da Sanata Natasha Akpoti da aka fi neman labaransu a 2025. Hoto: @MBuhari, Natasha H Akpoti/Facebook
Source: Twitter

Rahoton Google kan labaran da aka fi nema

Google ya ce binciken sunan Natasha da aka yi a 2025 ya zarce yadda aka saba gani, musamman saboda yawaitar tattaunawa da muhawara a kafafen yada labarai, in ji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna 2025 ta kasance shekara mai cike da abubuwan da suka dauki hankali, daga rikicin Isira’ila da Iran, zuwa zaben Amurka.

A Najeriya kuwa, mutane sun yi bincike sosai kan rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda suka duba tarihin mulkinsa da tasirin da ya bari.

Wasu sun koma duba labarai kan shahararren dan kwallon Super Eagles, Peter Rufai, wanda mutuwarsa ta sa aka nemi bayanai sosai kan rayuwarsa da gagarumar gudummawar da ya bayar.

Nishadi ya mamaye abubuwan da aka fi nema

Bangaren nishadi ya yi fice sosai a 2025, kamar yadda rahoton Google ya nuna cewa:

  • Waƙar yabon Yesu, “Oluwatosin (Jesus Is Enough)” ta Tkeyz ft. Steve Hills ita ce aka fi bincike; sai kuma wakar “Joy Is Coming” ta Fido da “With You” ta Davido ft.Omah Lay.
  • A fina-finai kuma, daraktar Nollywood Kemi Adetiba ta kasance cikin jerin sunayen da aka fi bincikensu, musamman saboda fim dinta, "To Kill a Monkey", wanda Google ya ce shi ne mafi bincike a Najeriya a 2025.

Kara karanta wannan

Yadda kashe Musulmai a Gaza ke saka turawa shiga Musulunci

‘Labubu’ da sauran kalmomin da suka yi tashe

Google ya ce yan Najeriya sun yi bincike kan al’adu da fahimtar wasu kalmomin da aka rika amfani da su a intanet a 2025, cewar rahoton The Nation.

Tambayar “Menene Labubu?” ita ce ta fi komai yawa. Har ila yau, kalmar 'Achalugo', wacce ta taso daga fina-finan YouTube, ta samu bincike sosai.

Tsokacin Google kan abin da binciken ya nuna

Manajan sadarwa na Google a shiyyar Yammacin Afrika, Taiwo Kola-Ogunlade, ya ce rahoton ba wai ya shafi iya bayanai ba ne, ya kuma zama madubin abin da zuciyar jama’a ke nema.

Taiwo Kola-Ogunlade ya ce:

“Mutane na amfani da Google wajen bibiyar abubuwan da suke son gani, koyon sababbin al’amura, da fahimtar duniya baki ɗaya.”

Google 2025: Abubuwan da suka yi fice a Nigeria

Sanata Natasha ce mafi shahara a 'yan Najeriya da aka rika neman sunansu a Google a 2025.
'Yar majalisar dattawa ai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti. Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook

Labaran da aka fi karantawa:

  • Club World Cup
  • Diogo Jota
  • Buhari
  • Israel–Iran War
  • Natasha Akpoti
  • Peter Rufai
  • iPhone 17

Mashahuran 'yan Najeriya:

  • Natasha Akpoti
  • Eberechi Eze
  • Fubara
  • Chika Ike
  • Hilda Baci
  • Kemi Adetiba

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun gwabza kazamin fada da ƴan bindiga a Abuja, an samu asarar rayuwa

Mutuwar mutanen da aka fi bincike:

  • Buhari
  • Peter Rufai
  • Diogo Jota
  • Hulk Hogan
  • Pope Francis

Tinubu zai hada hannu da Google

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na son hada hannu da kamfanin Google wajen samar da ayyukan yi.

Tinubu ya ce katafaren kamfanin na da cikakkiyar fasaha da abubuwan da ake bukata na kayan aiki don samar da ayyukan yi a Najeriya.

Mataimakin shugaban Google, Richard Gingras, ya ce Najeriya na da yawan jama'a da ake bukata domin fitar da sababbin fasahohin zamani.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com