Soyayya Ta Ƙare: Fitaccen Ɗan Crypto a Arewa, Ahmed XM Ya Yi wa Matarsa Saki 3

Soyayya Ta Ƙare: Fitaccen Ɗan Crypto a Arewa, Ahmed XM Ya Yi wa Matarsa Saki 3

  • Bayan dogon lokaci ana jita-jita a kafafen sada zumunta, a ranar Lahadi Safiya Umar ta bayyana cewa ta rabu da mijinta Ahmad XM
  • Safiya ta ce amayar da abin da yake cikinta shi ne kawai zai kawo karshen rade-radin da yawan tambayoyin da ake yi mata a halin yanzu
  • Lauyanta, Barista Hamza Dantani ya ce XM ya yiwa Safiya saki uku tun watanni biyar da suka wuce, kuma tana da sha'awar sake aure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Masana falsafa suka ce kamar sauran abubuwa masu rai, 'to shi ma aure rai gare shi,' domin yana da farko kuma yana da karshensa.

A karshen makon jiya, kafofin sada zumunta suka cika da labarin mutuwar auren fitaccen dan crypto na Arewa, Ahmed XM da matarsa Safiya Umar.

Kara karanta wannan

Ruwa zai yanke: NiMet ta saki sunayen jihohi 6 da za su fuskanci fari a Agusta

Aure tsakanin Ahmed XM da Safiya Umar ya mutu
Fitaccen dan crypto Ahmed XM tare da (tsohuwar) matarsa lokacin radin sunan diyarsu, Noor. Hoto: ahmed_xm_/Instagram
Asali: Twitter

Safiya Umar, a shafinta na Instagram ta sanar da cewa yanzu ba ta tare da mijinta Ahmed XM, don haka taga dacewar ta fito ta sanar da mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba na tare da Ahmad XM" - Safiya

Matashiyar ta ce sanar da duniya cewa aurenta ya mutu ba abu ne mai sauki ba, amma la'akari da cewa babu inda ba a san da zancen aurensu ba, ta ga dacewar ta fayyace komai.

A cewar Safiya, watau maman Noor:

"A yau na ga dacewar in fito in fayyace abin da ke zuciyata, in kuma ba da amsar da aka dade ana tambaya ta game da ko har yanzu ina tare a mijina.
"Ko kadan abubuwa ba su zo mun da sauki ba, amma ina mai bakin cikin sanar da ku cewa ba na tare da tsohon mijina, Ahmad Xm. Wannan jarabawa ce ta rayuwa.
"Ga wadanda suka karfafa mun gwiwa, suka yi mun addu'a, kuma suka nuna mun kauna, ba ni da bakin magana sai dai na ce na gode matuka."

Kara karanta wannan

Cin amana: Magidanci ya kama matarsa tsirara da wani namiji a gado, ya ɗauki mataki

Saki nawa Ahmad XM ya yiwa Safiya?

'Yan awanni bayan fitar bayanan Safiya, kafofin sada zumunta suka amsa sosai, inda mutane ke bayyana ra'ayoyinsu game da rabuwar auren.

Watakila, ganin yadda kura ta tashi ne ya sa Safiya ta amincewa lauyanta, Hamza Nuhu Dantani ya fito ya yi karin haske kan lamarin.

Barista Hamza Dantani ya bayyana cewa Ahmed XM ya yi wa Safiya saki 3 watanni 5 baya.
Barista Hamza Dantani ya yi karin haske game da mutuwar auren Ahmed XM da Safiya Umar. Hoto: Hamza Nuhu Dantani/ Facebook, Oumnoor/ Instagram.
Asali: Facebook

A shafinsa na Facebook, Barista Hamza Dantani ya ce:

"Da amincewar Safiya (tsohuwar matar XM), a matsayina na lauyanta, na fito domin in yiwa mutane bayani, duk da cewa a baya ta fitar da sanarwa game da hakan a shafinta na Instagram.
"Aurenta (Safiya) ya mutu tun kusan watanni biyar baya, kuma saki uku ne aka yi. Dalilin fayyace komai shi ne tana so ta yi wani auren.
"Boye wannan maganar ya jefa ta cikin kadaici, damuwa da kuma yi mata shamaki daga kulla soyayya da wani namiji, don kowa yana daukar cewa ita matar aure ce.

Kara karanta wannan

Jarumar fim, Ummi Nuhu ta fadi yadda ta nemi a yanke mata kafa bayan karaya 4

"Abun ya saka ta cikin damuwa ne, kuma tana son yin aure. Amma kowa yana mata kallon cewa tana da aure, kuma ita yarinya ce matashiya. Abun dai babu dadin bayani kawai."

Adam Zango ya gama zaman aure

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jarumi Adam Zango ya saki bidiyon da ya gigita masoyansa inda yace zai rabu da matarsa da yake aure yanzu.

Adam A Zango ya sanar da cewa, matarsa ta fifita kasuwancinta fiye da aurensa don haka ya gama aure tunda dama yana da zuri'a da yara.

A cewar jarumin da aka yi wa tambari da auri-saki, yace saboda yana fitacce ba zai cigaba da hadiyar bakin cikin ba yana kannewa saboda masoyansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel