Musulmai Sun Girgiza: Malami a Duniyar Musulunci, Sheikh Al Huwaini Ya Rasu

Musulmai Sun Girgiza: Malami a Duniyar Musulunci, Sheikh Al Huwaini Ya Rasu

  • Babban malamin Musulunci a duniya, Sheikh Abu Ishaq Al-Huwaini ya rasu yana da shekara 69 bayan fama da jinya
  • Rahotanni sun nuna cewa Al-Huwaini ya kasance mashahurin malami a fannin Hadisi da ya karantar a kasar Masar
  • Biyo bayan sanarwar rasuwar Sheikh Al-Huwaini, malamai da makarantun addini sun bayyana jimaminsu game da rashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Egypt - An shiga jimami a ƙauyen Huwin da ke Masar bayan rasuwar malamin Musulunci, Sheikh Abu Ishaq Al-Huwaini, a ranar Litinin.

Dansa, Haitham Al-Huwaini, ya bayyana cewa mahaifinsa ya rasu ne bayan da lafiyarsa ta kara tabarbarewa sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da shi.

Al-Huwaini
Sheikh Abu Ishaq Al-Huwaini ya rasu. Hoto: Haitham Al-Huwaini
Asali: Facebook

Haitham Al-Huwaini ya wallafa a Facebook cewa an garzaya da Malamin asibiti domin yi masa magani, amma bayan wasu awanni, ya rasu a ranar 17 ga watan Ramadan 1446 AH.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya rama miyagun maganganu da El Rufa'i ya fada masa a baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tarihin rayuwar Abu Ishaq Al-Huwaini

An haifi Sheikh Abu Ishaq Al-Huwaini a ranar 10 ga watan Yuni, 1955, a ƙauyen Huwin da ke lardin Kafr El-Sheikh a Masar.

Jaridar Egypt Today ta wallafa cewa ya yi fice a fannin karantarwar Hadisi da koyar da sunnonin Manzon Allah (S.A.W), kuma yana daga cikin manyan malaman Salafiyya a Masar.

Al-Huwaini ya shahara wajen gabatar da wa’azi da kuma shirye-shiryen addini a tashoshin talabijina a tashar Al-Nas TV da kuma kulawa da shirye-shiryen tashar Al-Rahma TV.

A tsawon rayuwarsa, ya kasance malami kuma jagora a fannin Fiqhu da Aqeedah, inda ya karantar da dubban dalibai a Masar da sauran kasashe.

Har ila yau, ya halarci tarukan ilimi da suka shafi addini a Masar da kasashen ketare, inda yake gabatar da jawabai kan mahimman al’amuran addini.

Haitham
Dan Sheikh Al-Huwaini, Haitham. Hoto: Haitham Al-Hawaini
Asali: Facebook

Gudunmuwar Al-Huwaini ga addinin Musulunci

Kara karanta wannan

Hatsabiban 'yan bindiga 18 da aka kashe a 2025 da tasirin hakan ga tsaron Arewa

Sheikh Abu Ishaq Al-Huwaini ya bayar da gagarumar gudunmuwa a fagen ilimin addini, musamman ta hanyar wa’azi da shirye-shiryen addini.

Rahoton kafar Watan ya nuna cewa daga cikin muhimman gudunmuwarsa akwai:

  • Gabatar da shirin “Fadfada” da ke tattauna batutuwan addini da zamantakewa.
  • Jagorantar shirye-shiryen tashar Al-Rahma TV domin yada ilimin addini.
  • Halartar tarurrukan addini da suka hada da haduwar manyan malaman Musulunci.

Bayan rasuwarsa, an bayyana jimami a kafafen sada zumunta, inda dubban mabiyansa suka nuna alhini kan wannan babban rashi.

Malamai da manyan cibiyoyin addini a Masar, ciki har da Al-Azhar, sun bayyana cewa rasuwarsa babban rashi ne ga al’ummar Musulmi.

Jimami da shirye-shiryen jana’izar Al-Huwaini

Jami'ar Al-Azhar, babbar makarantar ilimin addini a Masar, ta bayyana alhini kan rasuwar Sheikh Al-Huwaini, tana mai cewa ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimi.

Kara karanta wannan

Albarkacin azumi: Yadda almajirai suka yi cudanya da gwamnan Nasarawa

Dubban mutane ne ake sa ran za su halarci jana’izarsa, za a yi addu’o’i tare da tunawa da gudunmuwar da ya bayar a fannin addini.

A yau Talata za a gudanar da jana'izar malamin bayan sallar La'asar kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Sheikh Al-Huwaini ya bar dimbin dalibai da mabiyan da za su ci gaba da yadawa da koyar da ilimin da ya bari.

Sheikh Gumi ya yi martani wa El-Rufa'i

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani ga Nasir El-Rufa'i kan wasu maganganu da tsohon gwamnan ya taba fada a kansa.

Malamin ya ce yanzu lokaci ya yi da zai rama miyagun maganganu da tsohon gwamnan jihar Kaduna ya fada game da shi a shekarun baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng