Sheikh Guruntum Ya ba da Mamaki, Ya Ƙi Karbar Kyautar Miliyoyi daga Wani Alhaji
- An bayyana yadda Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya ki karbar kyautar Naira miliyan 10 da aka yi masa
- Kyautar ta fito ne daga wani mai kudi da aka roka ya bayar a lokacin auren ‘ya’yan Sheikh Guruntum da aka yi kwanaki
- Biyo bayan bayyanar lamarin, jama’a sun tofa albarkacin bakinsu, wasu na yabawa, wasu na nuna mamaki sosai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya ki karbar kyautar Naira miliyan 10 da aka ba shi a lokacin da ‘ya’yansa uku ke yin aure.
Shugaban hukumar alhazai ta kasa, Sheikh Abdullahi Sale Pakistan, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa irin wannan hali yana da wuyan samu a wannan zamanin.

Asali: Facebook
Lamarin ya bayyana ne a wani bidiyo da Abdullahi Suraj Nagegime ya wallafa a shafinsa na Facebook Sheikh Pakistan na bayanin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan wannan batu ya karade kafafen sada zumunta, mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu, wasu na yabawa Sheikh Guruntum bisa wannan.
Yadda aka so ba Sheikh Guruntum kyauta
A cewar Sheikh Pakistan, wani mutumi ne ke waya da Sheikh Guruntum yayin da wani mai hannu da shuni ya gayyace shi shan ruwa a gidansa.
Mutumin da ke waya da Sheikh Guruntum ya ba mai kudin labarin auren ‘ya’yan Malamin, tare da neman ya bayar da gudunmawa.
Mai kudin ya amince da bayar da Naira miliyan 10 a matsayin kyauta, amma da aka sanar da Sheikh Guruntum sai ya ki karba.

Asali: Facebook
Sheikh Pakistan ya ce, irin wannan hali yana da matukar wahala a samu a wannan lokaci, idan an samu ma ya ce za su zamo 'yan kadan ne.
Ya kuma yi wa Sheikh Guruntum fatan alheri tare da yabawa da irin halinsa na rikon amana da kyakkyawar dabi’a.
Martanin jama’a kan rashin karbar kudin
Bayan da Abdullahi Suraj Nagegime ya wallafa wannan batu, jama’a sun yi martani iri-iri kan lamarin.
Wani mai suna Buharee Baba Ali ya bayyana cewa:
"Wallahi irin halinsa kenan, ko zakka aka kawo wa Malam ba ya karba, domin shi ma yana cirewa.
"Wannan ne dalilin da yasa Allah ya sanya albarka a da’awarsa, kusan duk duniyar Hausa babu wanda ake sauraran karatunsa irin sa."
Shi ma wani mai suna Ishaq Yerima ya ce:
"Har nayi shirin yin raddi, saboda yadda ya fara magana kamar zai kushe Malam ne, ashe yabon Malam zaiyi.
"Shi ya sa mu daina gaggawar yanke hukunci. Allah ya yi jagoranci ga Malaman Sunnah, Ameen!"
A nasa martanin, Abubakar Muhammad Adam ya ce:

Kara karanta wannan
Duniya ta zo karshe: Annabin karya ya sake bayyana a Najeriya, ya ce ya ga Allah da idonsa
"Wallahi shiyasa muke ƙaunarsa. Bawan Allah kyauta ce fa! Ba roƙa yayi ba, kyauta aka masa amma inaaaaa! Malam Allah ya saka maka da Aljannatul Firdaus."
Lamarin Sheikh Guruntum na ci gaba da jawo martani daga jama’a, inda da dama ke ganin irin wannan hali yana da matukar wahala a samu a yau.
Sheikh Guruntum ya fara tafsiri a sabon masallaci
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya bude sabon masallacin juma'a a jihar Bauchi.
Biyo bayan bude masallacin, Sheikh Guruntum ya fara gabatar da tafsirin azumin watan Ramadan na shekarar 2025 a wajen.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng