Najeriya @64: Ahmadu Bello da Wasu Mutane 9 da Suka Yi Fafutukar Samun ‘Yanci
Abuja - A ranar Talata 1 ga watan Oktoba ne Najeriya da 'yan kasarta za su gudanar da bukukuwan murnar cika shekaru 64 da samun 'yanci daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abubuwa da yawa sun canza a cikin shekaru 64, musamman siyasar kasar. Sai dai abu daya da ba za a manta ba shi ne mutanen da suka yi fafutukar samun 'yanci.
Jagororin neman 'yancin kai a Najeriya
Daga Abubakar Tafawa Balewa, firaministan farko a Najeriya zuwa Nnamdi Azikiwe, zababben shugaban kasa na farko, mutane da dama sun sadaukar da rayukansu domin 'yancin kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar kullum, Legit Hausa na alfahari da su, a yayin da muka tattaro bayanan 10 daga cikin 'yan mazan jiya da fafutukarsu ta samar da 'yancin kan kasar nan.
1. Sir Abubakar Tafawa Balewa
Abubakar Tafawa Balewa ya kasance Firaminista na farko kuma daya tilo a Najeriya bayan samun ‘yancin kai.
Marigayi Abubakar Tafawa Balewa ya kasance babban mai kare muradun Arewa kuma mai fafutukar kawo sauyi da hadin kan Najeriya.
Tafawa Balewa na daya daga cikin wadanda suka yi fafutukar samun ‘yancin kan Najeriya a shekarar 1960.
2. Nnamdi Azikiwe
Marigayi Nnamdi Azikiwe wanda aka fi sani da Zik din Afrika, dan siyasa ne kuma jagoran juyin juya hali wanda ya zama gwamna na uku kuma bakar fata na farko a Najeriya daga 1960 zuwa 1963.
Nnamdi Azikiwe ne shugaban kasar Najeriya na farko a jamhuriya ta farko (1963-1966).
Ana yi masa kallon uban kishin kasa a Najeriya sannan kuma ya na daya daga cikin wadanda suka yi fafutukar samun ‘yancin kai a shekarar 1960.
3. Sir Ahmadu Bello
Ahmadu Bello (marigayi), wanda aka fi sani da Sardaunan Sokoto, dan Najeriya ne mai ra'ayin mazan jiya kuma ya kasance daya daga cikin manyan 'yan siyasar Arewa a 1960.
Sardauna Bello ya zama Firimiyan Arewa na farko kuma daya tilo daga 1954 har zuwa lokacin da aka kashe shi a shekarar 1966.
4. Obafemi Awolowo
Marigayi Obafemi Awolowo ya taka muhimmiyar rawa a yunkurin samun ‘yancin kai a Najeriya (1957–1960).
Tsohon dan jarida, Awolowo ya kafa kungiyar Yarbawa ta Egbe Omo Oduduwa, kuma shi ne Firimiyan farko a yankin Yamma karkashin tsarin majalisar dokokin Najeriya, daga 1952 zuwa 1959.
Ya kasance shugaban 'yan adawa a majalisar tarayya a lokacin gwamnatin Sir Abubakar Tafawa Balewa daga 1959-1963.
5. Margaret Ekpo
Margaret Ekpo ta kasance ‘yar siyasa ta farko a jamhuriya ta daya kuma ita ce jagorar rukunin mata masu fafutuka na gargajiya a Najeriya.
Marigiya Margaret ta taka rawa sosai a matsayinta na ’yar siyasa mai kishin kasa a birnin Aba da ke gabashin Najeriya, a lokacin da aka yi yunkurin neman ‘yancin kai.
6. Herbert Macaulay
Daga cikin wasu sana'o'i da ayyukan da ya kware a kansu, Herbert Macaulay ya kasance injiniya ne kuma ɗan jarida.
Mutane na yiwa Herbert Macaulay wanda ya rasu a shekarar 1946 kallon mutumin da ya karfafa kishin kasa a Najeriya.
7. Anthony Enahoro
Marigayi Anthony Enahoro ya kasance daya daga cikin jiga-jigan masu adawa da mulkin mallaka kuma mai neman samar da dimokradiyya a Najeriya.
Duk da koma bayar da ya samu a majalisar kasar, Enahoro ya fara gangamin jama'a domin ganin an taso da guguwar juyin juya hali daga masu mulkin mallaka.
8. Ernest Ikoli
Ana tunawa da Ernest Ikoli a tarihin Najeriya a matsayin daya daga cikin wadanda suka yi gwagwarmayar aikin jarida da kishin kasa.
Ikoli ne ya kafa kungiyar matasan Najeriya (NYM) a shekarar 1934 domin fafutukar neman yancin kai da mulkin dimokuradiyya daga turawan mulkin mallaka na Burtaniya.
Ernest Ikoli ya rasu a shekara ta 1960.
9. Eyo Ita
Eyo Ita masanin ilimi ne kuma dan siyasa daga garin Creek, a jihar Cross River a yau, wanda shi ne shugaban gwamnatin Gabashin Najeriya a 1951 kuma Farfesa na farko a Najeriya.
Ya kasance daya daga cikin daliban Najeriya na farko da suka yi karatu a Amurka maimakon karatu a Birtaniya da 'yan kasar suka saba.
10. Funmilayo Ransome-Kuti
Marigayiya Funmilayo Ransome-Kuti ta kasance malama kuma mai fafutukar kare hakkin mata.
Ita ce mahaifiyar marigayi Fela Anikulapo-Kuti, majagaba a wakokin Afrobeat.
Tinubu zai yiwa 'yan Najeriya jawabin bikin 'yanci
A wani labarin, mun ruwaito cewa Bola Ahmed Tinubu zai yi wa 'yan Najeriya jawabi kai tsayea ranar Talata, 1 ga watan Oktoban 2024.
Shugaban kasar zai yi jawabin ne da misalin karfe 7:00 na safe a wani bangare na bikin cika shekara 64 da samun 'yancin kan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng