Waiwaye: Jerin mutane bakwai da suka yi gwagwarmayar kwatowa Najeriya 'yanci daga hannun turawan mulkin mallaka

Waiwaye: Jerin mutane bakwai da suka yi gwagwarmayar kwatowa Najeriya 'yanci daga hannun turawan mulkin mallaka

- Jaridar Legit ta gano jerin mutanen da suka taka rawar gani wajen kwato 'yancin Najeriya

- Hakan ya sanya muka ware mutane bakwai da suka yi zarra wajen wannan jan aiki na kwato Najeriya daga hannun turawa

1. Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto (12 Yuni 1910 - 15 Janairu 1966)

Waiwaye: Jerin mutane bakwai da suka yi gwagwarmayar kwatowa Najeriya 'yanci daga hannun turawan mulkin mallaka
Sir Ahmadu Bello
Asali: Facebook

Sir Ahmadu Bello (Sardaunan Sokoto) dai an haife shi a garin Rabbah na jihar Sokoto dake yankin arewacin Najeriya. Sir Ahmadu Bello yana daya daga cikin mutane bakaken fata da suka yi fice a duniya. Sir Ahmadu Bello an bashi sarautar Sardaunan Sokoto, sannan ya rike shugaban jam'iyyar Northern People's Congress (NPC) a lokacin jamhuriya ta daya.

Sardauna yayi fadi tashi wajen kwatowa Najeriya 'yanci. A yanzu haka hoton Sardauna ne a jikin naira dari biyu (N200) ta Najeriya.

Kadan daga cikin abubuwan dake sanyawa a dinga tunawa da Sir Ahmadu Bello sun hada da babbar jami'ar Ahmadu Bello dake garin Zaria.

2. Cif Anthony Enahoro (22 Yuli 1923 - 15 Disamba 2010)

Waiwaye: Jerin mutane bakwai da suka yi gwagwarmayar kwatowa Najeriya 'yanci daga hannun turawan mulkin mallaka
Chief Anthony Enahoro
Asali: Facebook

Cif Anthony Eromosele Enahoro yana daya daga cikin mutanen da suka nuna rashin son turawa da mulkin mallakar da suka yi a wancan lokacin, sannan yana daya daga cikin mutanen da suka yi kokarin kafa dimokradiyya.

Enahoro ya fara aiki da jaridar Southern Nigerian Defender ta Nnamdi Azikiwe, yayin da ya zama ma'aikacin jarida mafi karancin shekaru a Najeriya a wancan lokacin. Enahoro ne mutum na farko da ya fara nuna bukatar nemawa Najeriya 'yancin kai a shekarar 1953. Wannan dalili ne ya sanya ake yi masa lakabi da 'Uban Najeriya'. Cif Anthony Enahoro dai yayi fafutuka a Najeriya har zuwa lokacin da ya mutu a shekarar 2010.

3. Herbert Macaulay (14 Nuwamba 1864 - 7 Mayu 1946)

Waiwaye: Jerin mutane bakwai da suka yi gwagwarmayar kwatowa Najeriya 'yanci daga hannun turawan mulkin mallaka
Herbert Macaulay
Asali: Facebook

Asalin sunansa shine Olayinka Herbert Samuel Heelas Badmus. Injiniya ne mai ilimi na tsara gine-gine, sannan dan jarida ne kuma yana taba harkar waka. Mutum ne shi mai kishin kasa da kuma ra'ayi na siyasa. Mutane da yawan gaske a Najeriya suna yi masa lakabi da jagoran masu kishin Najeriya.

Herbert Macaulay yayi kaurin suna wajen rikici da turawan mulkin mallaka. Inda a shekarar 1919 ya taya wasu Sarakuna a kasar Landan wadanda aka kwacewa gonaki ya tilasta turawa suka biya wadannan mutane diyya.

Wannan dalili ne ya sanya majalisar kasar Birtaniya ta kama shi ta sanya a gidan yari. A ranar 24 ga watan Yuni 1923 Herbert Macaulay ya kafa jam'iyyar siyasar sa ta farko mai suna Nigerian National Democratic Party (NNDP). Herbert Macaulay ya mutu a shekarar 1946, inda aka anya hotonsa a tsohuwar naira daya (N1) domin a dinga tunawa dashi.

4. Cif Obafemi Awolowo (6 Maris 1909 - 9 Mayu 1987)

Waiwaye: Jerin mutane bakwai da suka yi gwagwarmayar kwatowa Najeriya 'yanci daga hannun turawan mulkin mallaka
Chief Obafemi Awolowo
Asali: UGC

Cif Obafemi Oyeniyi Awolowo mutum ne mai kishin kasa, sannan kuma cikakken dattijo wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen nemawa Najeriya 'yancin kai. Shi ne firimiyan yankin kudu maso yammacin Najeriya na farko, sannan kuma ya rike mukamin kwamishinan kudi a gwamnatin tarayya. Haka kuma Cif Obafemi Awolowo ya kasance mataimakin shugaban kasa a majalisar zartarwa a lokacin da ake yakin basasa. Duk da cewa bai samu nasarar lashe zaben shugaban kasa a lokacin jamhuriyya ta biyu ba, Obafemi Awolowo ya kasance dan takara na biyu mai yawan kuri'u banda Alhaji Shehu Shagari. Hoton shi ne a jikin naira dari ta yanzu (N100).

5. Funmilayo Ransom Kuti (25 Oktoba 1900 - 13 Afrilu 1978)

Waiwaye: Jerin mutane bakwai da suka yi gwagwarmayar kwatowa Najeriya 'yanci daga hannun turawan mulkin mallaka
Funmilayo Ransom Kuti
Asali: Facebook

Funmilayo Ransom Kuti ta kasance mace guda daya tilo da ta fito a cikin jerin sunayen masu fafutukar nemawa Najeriya 'yanci. Ita dai ta kasance malamar makaranta ce, 'yar siyasa, sannan kuma mai fafutukar kare hakkin mata, haka kuma tana rike da sauratar gargajiya. Ita ce mahaifiyar shahararren mawakin nan na Najeriya, Femi Kuti wanda aka fi sani da Fela. Ita ce mace ta farko da ta fara tuka mota a Najeriya.

6. Nnamdi Azikwe (16 Nowamba 1904 - 11 Mayu 1996)

Waiwaye: Jerin mutane bakwai da suka yi gwagwarmayar kwatowa Najeriya 'yanci daga hannun turawan mulkin mallaka
Dr Nnamdi Azikwe
Asali: Facebook

Cif Benjamin Nnamdi Azikwe shine shugaban masu gwagwarmayar kishin kasa na zamani. Cif Nnamdi Azikwe ya rike edita na jaridar Morning Post. Shi ne mutum na farko dan Najeriya da sunansa ya fara shiga majalisar Amurka. Bayan bayyana Najeriya a matsayin jamhuriya, yayi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya hada kan al'ummar Najeriya. Shine kuma ya zamo shugaban Najeriya na farko.

7. Sir Abubakar Tafawa Balewa (Disamba 1912 - 15 Janairu 1966)

Waiwaye: Jerin mutane bakwai da suka yi gwagwarmayar kwatowa Najeriya 'yanci daga hannun turawan mulkin mallaka
Sir Abubakar Tafawa Balewa
Asali: Facebook

Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa shine firai ministan Najeriya na farko, bayan kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 1960. Sannan kuma an zabe shi a matsayin dan majalisar yankin arewa a shekarar 1946. Haka kuma yaje majalisar dokoki ta tarayya a shekarar 1947. Sir Abubakar Tafawa Balewa ya zama dan majalisa mai rajin kare yankin arewa. Sun kafa jam'iyyar Northern People's Congress (NPC) shi da Sardaunan Sokoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng