A rana mai kamar ta yau a Tarihi, Firai Minista Tafawa Balewa ya hau mulki a 1957, shekaru uku kafin samun 'yancin kai
- Shekara 60 kenan da suka wuce a rana ita yau, ranar 30, ga watan 1957, Abubakar Tafawa Balewa ya hau mulkin Firai Minista a Najeriya
An haifi Abubakar Balewa a shekarar 1912 a Balewa, da ke Bauchi. Ya fara Islamiyya kafin ya shiga makarantar boko a Bauchi Provincial School. Bayan makarantar firamare sai kuma ya tafi Katsina Teacher Training College daga 1928 zuwa 1933.
Da ya gama nan kuma sai ya zama malami, sannan daga nan ya zama shedimastar Bauchi Middle School. A 1945 ne ya sami tallafin turawa ya tafi Jami’ar Landan ya karanci tarihi.
Balewa ya shiga gwamnati a ministan aikace-aikace a 1952. Daga nan kuma ya zama ministan harkokin sufuri. A 1957 ya zama shugaban NPC. Da aka samu ‘yancin kasa jamiyyar sa ta samu kujerun majalisa da dama shine ya zama firaminista. Haka kuma aka sake zaben sa a zaben 1964.
DUBA WANNAN: Abinci ya fara tsada a Kasuwanni, Shugaba Buhari ya fara daukar mataki
A watan Janairu shekarar 1966 ne aka kashe shi a ku din da aka yi a karkashin soja Kaduna Nzegwu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng