Jarumar Fim Ta Fallasa ‘Alaƙar’ da Ke Tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio

Jarumar Fim Ta Fallasa ‘Alaƙar’ da Ke Tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Akpabio

  • Jarumar Nollywood, Dakore Egbuson-Akande ta musanta labarin da ke yawo na cewa tana mu'amala da shugaban majalisar dattawa
  • Ta bayyana rade-radin matsayin muguwar ƙarya wacce wasu masu son bata mata suna suka shirya, kuma ta ɗauka matakin shari'a
  • 'Yar wasar ta buƙaci duk mai bidiyo ko sautin muryarta da wani namiji da ya garzayo ya kawo, za ta bayar da tukuicin Naira miliyan biyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jaruma Dakore Egbuson-Akande ta musanta zargin da ake yaɗawa kan cewa akwai wata alaƙar soyayya tsakaninta da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

A baya bayan nan wasu kafofin sada zumunta suka ruwaito cewa Egbuson-Akande tana daya daga cikin 'yan matan Sanata Akpabio da suke holewa.

Kara karanta wannan

N70,000: Ƴan aikin gida za su sha romo, majalisa da ƙungiyar NCWS sun miƙa bukata

Jarumar Nollywood, Dakore Egbuson-Akande ta yi magana kan alakarta da Sanata Akpabio
Jarumar Nollywood ta karyata masu cewa tana soyayya da shugaban majalisar dattawa. Hoto: @SPNigeria, @AkandeDakore
Asali: Twitter

Jarumar fim ta karyata sanin Akpabio

A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram, Egbuson-Akande ta kwatanta zarge-zargen a matsayin "muguwar ƙarya" kuma ta nuna mamakinta da takaici.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kai-tsaye ta musanta cewa ta taba ganin Akpabio ido da ido, inda ta bayyana cewa bata taba zama ɗaki ɗaya da shi ba.

Egbuson-Akande, wacce ke da aure har da 'ya'ya biyu, ta ƙalubalanci masu yaɗa rade-radin da su zo da shaida inda ta ce zata bayar da tukuicin Naira miliyan biyar.

Ta jaddada mayar da hankalinta wurin kare sunanta tare da barazanar ɗaukar matakin shari'a kan duk waɗanda suka fara yaɗa zarge-zargen.

Jarumar fim za ta garzaya kotu

Kamar yadda jarumar ta ce:

Dole ne in ce na ji kunya, mamaki da firgici. Kuma ina son sanar da ku cewa ban taɓa haduwa da shugaban majalisar dattawa ba a rayuwata."

Kara karanta wannan

Fulani makiyaya za su shiga zanga zangar adawa da Tinubu? Miyetti Allah ta magantu

"Ban taba samun dalilin da zai sa mu zauna ɗaki ɗaya da shi ba balle in zama budurwarsa ta holewa. Ina da aure mai cike da farin ciki da kyawawan yara biyu.
"Ƙarya ne aka shirya kuma na shirya ɗaukar matakin shari'a saboda a yanzu, kun taɓo wanda ba za ta hakura ba. Ina kiyaye kaina tare da kiyaye abin da ya shafe ni.

Fitaccen jarumin Kannywood ya rasu

A wani labari na daban, mun ruwaito muku cewa jarumin Kannywood Sulaiman Alaƙa ya kwanta dama a ranar 22 ga watan Yulin 2024.

Jarumin fitacce ne kuma ana ji da shi a masana'antar ta Arewacin Najeriya, lamarin da yasa abokan aikinsa suka dinga jimamin rashinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.