CP Salman Dogo: Abin da Muka Sani Game da Sabon Kwamishinan Ƴan Sandan Kano
Jihar Kano - A ranar Litinin, 24 ga watan Yunin 2024 sabon kwamishinan ƴan sanda da aka tura zuwa jihar Kano, CP Salman Dogo Garba ya kamata aiki.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
CP Salman Garba ya karbi ragamar rundunar ƴan sandan ne daga Usaini Gumel wanda aka karawa matsayi zuwa muƙamin mataimakin Sufeta Janar.
Kamar yadda muka ruwaito, CP Salman Garba ya lashi takobin yin aiki tuƙuru domin wanzar da zaman lafiya a Kano da kuma kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.
Abin da muka sani kan CP Salman Dogo
Kakakin rundunar ƴan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya zayyana wasu muhimman abubuwa game da rayuwar sabon kwamishinan a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Haihuwar CP Salman Dogo da karatu
An haifi CP Salman a ranar 21 ga watan Yulin 1996 a Ilorin ta Yamma da ke jihar Kwara. Ya yi karatun firamare a Al-Mubarak.
Ya yi karatun sakandare a kwalejin malamai ta Kabba, sannan ya garzaya jami'ar Ahmadu Bello, ina ya samu shaidar kammala digirin farko.
2. Shiga aikin ɗan sanda a shekarar 1992
CP Salman ya shiga aikin ɗan sanda a ranar 18 ga watan Mayun 1992 a matsayin C/ASP, kuma ya samu horo a makarantar ƴan sanda ta Kano.
An fara tura shi ofishin ƴan sanda na Garki a shekarar 1994.
3. Muƙaman da CP Salman Dogo ya riƙe
Daga shekarar 1995 zuwa 2014, ya rike mukamai da dama ciki har da: DCO, OC/SARS, DPO, SOS, CSP 'A', ACM, da kuma muƙamin AC na ofishin Wudil.
Daga shekarar 2019 zuwa 2024, CP Salman ya samu ƙarin girma zuwa muƙamin DCP (2019-2022); CP (2022-2024).
CP Salman ya yi aiki a jihohin Najeriya da dama ciki har da, Abuja, Delta, Osun, Legas, Kaduna, Anambra, Bauchi, da kuma Kano.
4. Kwasa-kwasan da CP Salman ya halarta
CP Salman ya halarci kwasa-kwasai da dama, ya halarci tarurrukan karawa juna sani, da tarurrukan ba da horo a ciki da wajen Najeriya.
Ya halarci kwas ɗin 'yan sanda a Amurka a 2008, a 1999 ya yi kwas a kwalejin 'yan sanda ta Jos, sannan ya yi kwas a makarantar jami'an sojin Najeriya da ke Legas a 2010.
A shekarar 2018 ya sake komawa kwalejin 'yan sanda ta Jos inda ya yi kwana kan sanin makamar shugananci.
Yan sanda sun mamaye fadar sarkin Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an rundunar 'yan sanda sun fatattaki 'yan tauri da ke gadin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a fadar Rumfa.
Bayan korar 'yan taurin, an ruwaito cewa yan sandan sun mamaye fadar sarkin tare da zama masu tsaron ta, a wani yunkuri da ake zargi na maido da Aminu Bayero fadar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng