Makarantar horar da ‘yan sanda ta Wudil ta sanya ranar jarabawar sabbin shiga

Makarantar horar da ‘yan sanda ta Wudil ta sanya ranar jarabawar sabbin shiga

-Makarantar horar da 'yan sanda ta Wudil za ta gudanar da jarabawar sabbin shiga ranar Asabar 24 ga Agusta

-Kakakin rundunar 'yan sandan Legas DSP Bala Elkana ne ya fitar da wannan sanarwa ranar Alhamis 22 ga watan Agusta

-Za a fara wannan jarabawar ne da misalin karfe 7 na safiyar Asabar kamar yadda ya fadi cikin sanarwar tasa

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta sanar da daliban da suka nemi samun gurbin karatu a makarantar horar da ‘yan sanda ta Wudil wato Nigerian Police Academy, Kano cewa za a rubuta jarabawar sabbin shiga a ranar Asabar 24 ga watan Agusta.

Majiyar da ta kawo mana wannan labarin ta ce kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas DSP Bala Elkana ne ya bada wannan sanarwar a ranar Alhamis 22 ga watan Agusta inda yake cewa cibiyoyi rubuta jarabawar a Legas sun hada da, Kwalejin ‘yan sanda ta Ikeja, Kings College da Makarantar mata ta Anwarul Islam.

KU KARANTA:Mamakon ruwan sama ya yi awon gaba da kananan yara 3 a jahar Kano

A zancen da rundunar da fitar ta sanar da masu rubuta jarabawar cewa kowa ya fidda katinsa na jarabawar a yanar gizo kuma dole ne mutum ya kasance a wurin rubuta jarabawar da karfe 7 daidai na ranar jarabawar.

Ga abinda zance yake fadi: “ Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas na farin cikin sanar da al’umma cewa Makarantar horar da ‘yan sanda ta Wudil za ta rubuta jarabawar sabbin shiga rukuni na 7 a ranar Asabar 24 ga watan Agusta.

“ Wuraren rubuta jarabawar su ne kamar haka, Kwalejin ‘yan sanda ta Ikeja, Kings College Obalende da kuma Makarantar mata ta Anwarul Islam.

“ Ana shawartar ko wane dalibin da zai rubuta wannan jarabawar da ya fitar da katinsa na rubuta jarabawa daga shafin yanar gizo. Sannan kuma kowa ya kasance a wurin rubuta jarabawar kafin karfe 7 na safiyar ranar Asabar.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel