Dubi irin abincin da sojoji ke ci a makarantar sojoji (hotuna)
- Sojoji a makarantar soja a Legas suna gunaguni game da jin dadin su
- Sun yi iƙirarin abincin da ake ba su ya na sa su rashin lafiya
- Sun yi kira ga shugaban sojojin ya duba
Sojoji da ke makarantar sojin na school of signals Najeriya a cikin Apapa sun kawo zargi Cewa shugabannin su na yaudarar su wajen abincin su.
A cikin wata rahoto na musamman zuwa Legit.ng, an bayar da rahoton cewa rashin abinci mai kyau yana sa wasu rashin lafiya bayan sun ci shi.
Sun kuma yi kira ga shugaban rundunar sojojin, Tukur Buratai, don duba batun.
Karanta rahoton da ke ƙasa
Makarantar rundunar sojojin Najeriya,makaranta ce na horar wa amma tsarin doka na cikin makarantar ya samu mummunan tsari. Inda hukumar tana samun kudi ta hanyar abincin sojojin makarantar.
Ina amfani da wannan damar don shugaban rundunar sojojin ya taimaka wa sojojinmu ta hanyar duba makarantar don sanin ko gaskiya ne ko karya ne.
KU KARANTA KUMA: Toh fa! Gungun yan fashi daga jihar Ebonyi sun yi musayar wuta da Ýansanda a Kano
Hoton da ke sama shi ne daya daga cikin abincin da suka ci a yau ..... mutane da dama suna rashin lafiya saboda rashin cin abinci mai kyau.
Daliban sun yi kuka ga kwamandan amma abubuwa sun ci gaba da tafiya kamar da. Muna rokon shugaban ma'aikatan soji don taimaka mana da wannan maganar abincin.
"Ko wasu sojoji da suka zo daga arewa maso gabas suna cewa abincin su yafi namu kyau,gashi farashin kayan abincin su,ya fi namu anan.
Albashin mu ba za ta iya ciyar da mu ba,ballantana sojan dake zama a wajen makaranta,kudin da gwamnati ta amince da ita don ciyar da mu shine wasu suke ci kuma suna karɓar albashi fiye da soja." Suka ce
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng