An Nada Wanda Idriss Deby Taba Kora a Matsayin Sabon Firaministan Chadi

An Nada Wanda Idriss Deby Taba Kora a Matsayin Sabon Firaministan Chadi

- Gwamnatin kasar Chadi ta yi nadin sabon Firaministan rikon kwarya a kasar bayan nadin shuagaban kasa

- An nada Albert Pahimi Padacké a matsayin Firaminista bayan mutuwar Idriss Deby a makon jiya

- Sai dai, Shugaban 'yan adawa na kasar Yacine Abderamane ya ki amincewa da nadin tare da fadin dalilinsa

Gwamnatin sojin kasar Chadi ta sanar da nada sabon Firaministan rikon kwarya wanda ya yi takarar shugabancin kasa a zaben da aka yi a wannan watan, BBC ta ruwaito.

An nada Albert Pahimi Padacké bayan mutuwar shugaban kasar Idriss Deby a makon jiya.

Mr Albert Pahimi Padacké ya rike matsayin Firaministan karkashin gwamnatin marigayi Deby kafin daga baya ya soke matsayin a 2018.

KU KARANTA: Haramun Ne Yin Kasuwancin Bitcoin, in Ji Shehin Malami Daga Kano

An Nada Wanda Idriss Deby Taba Kora a Matsayin Sabon Firaministan Chadi
An Nada Wanda Idriss Deby Taba Kora a Matsayin Sabon Firaministan Chadi Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Shugaban 'yan adawa na kasar Yacine Abderamane, ya ki amincewa da nadin, yana cewa gwamnatin rikon kwarya ba ta da hurumin yin irin wannan nadi.

An kashe Idriss Deby ne kwana guda bayan lashe zaben shugabancin kasar Lokacin da yake gwagwarmaya da 'yan tawaye da suka shiga Chadi daga Libya.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Hallaka Wani DPO da Jami’ansa 8 a Wata Jihar Arewacin Najeriya

A wani labarin daban, Yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad bin Salman bin Abdulaziz da mataimakin Firaminista da kuma ministan tsaro sun tattauna da shugaban sojin Chadi Mahamat Idriss Deby ta wayar tarho a ranar Lahadi.

Alarabiya News ta ruwaito cewa, Yarima bin Salman ya yi wa Janar Mahamat Deby ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa Idriss Deby wanda ya rasu a ranar Litinin sakamakon samun wasu raunuka a fagen daga.

A bayaninsa, Yariman ya yi wa Chadi fatan dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali. A nasa bangaren kuma Janar Mahamat ya gode wa Yariman kan karamcin da ya nuna masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.