Rashin Haihuwa: Matar Aure Ta Sayi Kayan Jarirai, Ta Wallafa Bidiyon Halin da Take Ciki

Rashin Haihuwa: Matar Aure Ta Sayi Kayan Jarirai, Ta Wallafa Bidiyon Halin da Take Ciki

  • Wata mata 'yar Najeriya ta fashe da kuka saboda jinkirin da take fuskanta na samun haihuwa tun bayan da ta yi aure
  • A cikin wani faifan bidiyo, an ganta rike da bulumboti, famfas da sauran kayayyakin jarirai da ta siya a yayin da take hawaye
  • A zantawarsa da Legit Hausa, Goni Abubakar Sa'id Funtua ya ce wadanda ke neman haihuwa su yawaita yin 'istigfari'

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wata matar aure ‘yar Najeriya ta ja hankalin ma'abota amfani da da shafukan yanar gizo bayan ta wallafa bidiyon halin da take ciki na rashin haihuwa.

A wani faifan bidiyo da ya karade soshiyal midiya, an ga matar tana zubar da hawaye tare da yin addu'ar ubangiji ya ba ta haihuwa.

Kara karanta wannan

"Shi ke haukata 'yan kasa", Malamin addini a Kaduna ya ja kunnen Tinubu kan halin kunci

Matar aure da ba ta taba haihuwa ta roki ubangiji ya sa ta dauki ciki
Wata matar aure ta koka kan rashin haihuwa, ta sayi kayan jarirai. Hoto: @dailydose/TikTok, Maria Toutoudaki / Getty Images
Asali: TikTok

Matar aure tayi kuka kan rashin haihuwa

A cikin bidiyon da aka wallafa a kan shafin TikTok na @dailydoseblogger, an ga matar auren rike da wasu kayayyaki da aka yi wa jarirai ciki har da famfas, bulumboti da tufafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yi amfani da kayan ne a yayin da take zubar da hawaye tana addu'a ga ubangiji bisa yakinin zai cika mata burin zuciyarta na samun ciki.

An tattaro cewa budurwar ta fuskanci hantara da wulakanci daga mutane kan jinkirin da ta samu na daukar ciki tun bayan aurenta.

'Yan Najeriya sun yi martani kan bidiyon

Masu amfani da soshiyal midiya da suka kalli bidiyon matar mai taɓa zuciya a kan TikTok sun shiga sashen sharhi sun yi martani kan bidiyon.

Yayin da wasu masu suka jajanta mata kan radadin da take ji, wasu kuma sun yi mata addu'ar Allah ya albarkace ta da samun ɗa.

Kara karanta wannan

Yadda matsalar ruwa ke haifar da wahalar rayuwa a Arewacin Najeriya

@nk ya ce:

"Ubangiji ina rokonka ka albarkaci wannan baiwar taka da jarirai, ina da yakinin za ka amsa wannan addu'ar."

@Nanacouture&fabrics ta ce:

"Allah zai ji kukan ki kuma ya baki yaro ko yara masu albarka, kada ki damu, ki dogara ga Allah, shi ne mai yin komai."

@AbiolaSundayAdeoye ya ce:

"Ubangiji zai albarkace ta da 'ya'ya nagari. Ta haifi 'yan biyu da zasu share mata hawaye."

@Omo_Salami:

"Ina rokon mahaliccinmu ya azurta dukkanin mata da samun haihuwa. Lallai samun ciki albarka ce da ba za ka iya saya ba sai dai Ubangiji ya ba ka."

@JoyOmojirhe ta yi sharhi:

"Ki share hawayen ki domin maganar Ubangiji ce kan yin kuka da daddare amma farin ciki ya biyo baya da safe. Za ki hayayyafa da izinin Ubagiji."

Kalli bidiyon a kasa:

Addu'ar neman samun haihuwa

Ko Legit Hausa ta tuntubi Goni Abubakar Sa'id Funtua ko akwai addu'ar neman haihuwa, malamin ya ce:

Kara karanta wannan

FAAN ta dauki matakin gaggawa da gobara ta tashi a filin jirgin saman Legas

"Akwai addu'o'i da dama da mutum zai yi, walau mace ko namiji, sai dai mafi girman addu'ar ita ce 'Istigfari'.
"Ga duk mai neman haihuwa, ya dage da neman gafarar Allah musamman a bayan Sallolin farilla. Babu wata musiba ko wata bukata da Allah ba ya gusarwa ko ba ya amsawa idan ana istigfari."

Goni Sa'id ya kuma yi kira ga al'umar Musulmi da su kasance masu kiyaye dokokin Allah, da yi masa biyayya, a cewar sa ta hakan ne zai shiga lamuransu.

Ango ya kunyata amarya gaban jama'a

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda wani ango yaki yarda ya sumbaci amaryarsa a wajen da ake gudanar da taron daurin aurensu.

Mahalarta taron sun cika da mamakin wannan hali na angon la'akari da cewa al'adar daurin aure ce ga mabiya addinin Kirista musamman tun da coci ne za a daura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.