Tsohuwar da bata samu haihuwa ba ta ce ita da kanta ta nema wa mijinta sabuwar mata

Tsohuwar da bata samu haihuwa ba ta ce ita da kanta ta nema wa mijinta sabuwar mata

- Margaret Wanjira ta kasance amarya mai cike da farin ciki a lokacin da ta auri mijinta

- Sai dai kuma, rashin haihuwa ya kawo cikas a aurensu sannan tana ta jure duk wani matsi daga wajen surukanta

- Wanja ta yanke shawarar samawa mijinta wata sabuwar mata wacce ta zo ta haihu

Mafi akasarin al’adun Afrika kan tsangwami matayen da basa haihuwa.

Wasu lokutan, har yan uwan miji kan fatattaki mata daga gidajen aurensu sannan su sama wa yaransu maza sabbin mata wadanda ke haihuwa.

Margaret Wanjira, wata mata da ta doshi shekaru 100 a yanzu, ta auri masoyinta a lokacin da take da kuruciya.

Tsohuwar da bata samu haihuwa ba ta ce ita da kanta ta nema wa mijinta sabuwar mata
Tsohuwar da bata samu haihuwa ba ta ce ita da kanta ta nema wa mijinta sabuwar mata Hoto: Monica Kagoni
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Jerin sunaye: Kasashe 44 da yan Najeriya za su iya zuwa ba tare da biza ba

Ta san cewa mijinta ne burin zuciyarta sannan tayi tunanin za su kasance tare muddin rayuwarsu.

Abunda bata kawo a ranta ba shine inda za su samu tangarda da sabanin da ka iya kunno kai a gaba.

Tsohuwar ta fada ma yar jarida Monica Kagoni cewa ta fuskanci matsaloli da dama daga yan uwan mijinta saboda rashin haihuwarta.

Har sai da tayi abunda hankali ba zai yi tunanin aikatawa ba don ganin aurenta ya rayu. Ta sama wa mijinta mata ta biyu.

Wanjira ta ce:

“Sai da na nema wa mijina matashiyar budurwa wacce za ta Haifa masa yara. Da farko ya turje, amma nayi barazanar barinsa idan bai aure ta ba. Ina kaunar kishiyata kuma harma muna bacci a daki daya.”

Tsohuwar ta ci gaba da bayanin cewa duk da ta kawo kishiya, surukan nata sun maishe ta abun ba’a amma sai tayi kokarin sanyawa zuciyarta salama.

Amma ta yi iya bakin kokarinta wajen so da kare matar da ta mayar da mijinta uba.

Wanjira na kwana a daki guda da kishiyarta sannan ta dauketa kamar yar’uwarta.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 4 da Shugaban ma’aikatan tsaro ya fada ma dakarun da ke fagen fama a Maiduguri

Ta kara da cewa:

“Na kaunaci kishiyata sosai kuma ban taba bari mijina ya muzguna mata ba. Mijina ya ci gaba da kasancewa mai adalci a gareni kuma yana mika mun albashinsa. Amma daga baya aka korani daga gidansa.”

Abunda ke dadawa Wanjira rai shine cewa mijinta na mata biyayya.

Harma ya yarda ya mika mata albashinsa gaba daya sannan kuma ita ce ke kula da ragamar kudinsa.

A wani labarin, yarinya mai wasan barkwaci, Emmanuella ta janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamani bayan ta wallafa wasu hotuna a shafinta na Instagram.

A hotunan, an ga yarinyar tare da wata kawarta suna tsaye bayan wata hadaddiyar mota suna yi wa masoyanta fatan alheri.

Hotunan sun bayyana wata mota kirar Lexus 570 mai darajar miliyoyin naira.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel