Hotunan aure: Bidiyon yadda amarya ta hana angonta ya sumbace ta saboda ta yi kwalliya

Hotunan aure: Bidiyon yadda amarya ta hana angonta ya sumbace ta saboda ta yi kwalliya

- Wata amarya ta basar a lokacin da mijinta ya yi kokarin sumbatar ta yayinda suke daukar hotunan aurensu

- Kyakyawar matashiyar ta fada ma angonta cewa kada ya lalata mata kwalliyarta

- Daga bisani sai amaryar ta bukaci mijin nata da ya yi kamar yana so ya sumbaceta

Bidiyon wata kyakyawar amarya ya sanya yan Najeriya da dama dariya a shafin soshiyal midiya. A bidiyon wanda Legit.ng ta samo a shafin Instagram, an gano amaryar da angonta suna ta dauke dauken hotunan auransu.

Mai daukarsu hoton ya bukaci angon ya mannawa amaryarsa sumba a kumatu amma sai ta yi gaggawan janyewa, inda ta fada wa mijin cewa kada ya taba mata kwalliyarta.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon yadda yan achaba suka fatattaki jami’an yan sanda a Lagas

Hotunan aure: Bidiyon yadda amarya ta hana angonta ya sumbace ta saboda ta yi kwalliya
Hotunan aure: Bidiyon yadda amarya ta hana angonta ya sumbace ta saboda ta yi kwalliya Hoto: @weddingdigestnaija
Asali: Instagram

Daga bisani sai kyakyawar amaryar ta bukaci mijin da yayi kamar yana so ya sumbaceta amma kada ya kusanceta sosai saboda kada ya bata mata kwalliyarta.

Abunda amaryar ta yi ya baiwa mutane dariya yayinda aka jiyo wasu muryoyi suna mata dariya a kasan bidiyon.

KU KARANTA KUMA: Allah ya azurta ma’auratan da suka yi shekaru 6 ba haihuwa da ‘yan uku shekaru 3 bayan sun karbi rikon wata yarinya

A wani labari na daban, Bashir El-Rufai, daya daga cikin yaran gwamnan jihar Kaduna, ya haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya bayan ya wallafa hotunansa da amaryarsa a kan Twitter.

A cikin hotunan, an gano Bashir rike da kugun amaryarsa yayinda ita ma ta kamo shi cike da kauna.

A wani hoto kuma, an gano Bashir yana sumbatar amaryarsa a kumatu yayinda ita kuma ta rike fuskarsa tana murmusawa.

Sai dai kuma hakan ya fusata musulmai da Hausawa da ke amfani da Twitter inda suka yi wa hakan kallon bai dace ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel