An sha ‘yar dirama yayin da amarya ta ki yarda ta sumbaci angonta, jama’a sun yi martani a kan bidiyon

An sha ‘yar dirama yayin da amarya ta ki yarda ta sumbaci angonta, jama’a sun yi martani a kan bidiyon

  • Wata amarya ta haddasa cece-kuce a shafukan sada zumunta sakamakon abin da ta aikata ba zato ba tsammani lokacin da ya kamata ta sumbaci ango
  • Ga mamakin baƙin da suka halarci wurin bikin, amaryar ta ƙi sumbantar mijinta duk da ƙoƙarin da ya yi
  • Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi tsokaci kan abun da matar tayi inda wasu ke cewa wata kila amaryar na jin kunya ne

Wata mata ta yi abin da ba a zata ba a bikin aurenta wanda ya haifar da cece-kuce a kafofin sada zumunta.

Wannan ya kasance ne yayinda amarya ta guji sumbatar mijinta lokacin da aka buƙaci hakan.

An sha ‘yar dirama yayin da amarya ta ki yarda ta sumbaci angonta, taron jama’a sun yi martani a bidiyon
Amaryar tana jin kunya Hoto: @mufasatundeednut
Asali: Instagram

Bayan faston da ya kasance madaurin auren ya bukaci angon da ya sumbaci amaryar tasa sai ta ki yarje masa.

A cikin bidiyon da @mufasatundeednut ya wallafa a Instagram, amaryar ta yi murmushi kadan wanda ya nuna tana jin kunya kuma ta ki tabuka komai duk da karfin gwiwar da baƙi ke bata na ta bi tsarin daurin auren.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: IBB ya bayyana manyan kalubale 2 da rundunar sojojin Najeriya ke fuskanta

Mutumin bayan ya kokarta ba tare da nasara ba sai ya goga lebensa akan nata.

Ba za a iya tantance wurin daurin auren ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Kalli bidiyon a ƙasa:

Shafukan sadarwa sun mayar da martani

@yetundebakare ta ce:

"Tana yi kamar an tilasta mata ko kuma ta yi wa wani karya.”

@funnymrpeter yayi sharhi:

"Ba ni da matsala da amaryar, DJ din ne matsalar a nan, me yasa zai saka irin wannan waƙar."

Wata Amarya Ta Hallaka Angonta Kwanaki Kadan Bayan Sun Yi Auren Soyayya

A wani labarin kuma, mun ji cewa an gano gawar wani ango a ƙasar Habasha kwanakin kaɗan bayan ɗaura masa aure a garin Nekemte dake yammacin Habasha.

Angon mai suna Gemechis Mosisa, ma'aikacin jinyane ɗan kimanin shekara 28, ya wallafa sakon aurensa a dandalin sada zumunta na facebook ranar Asabar.

Bayan kwana ɗaya, wato ranar Lahadi Mosisa ya sanya hotunan shagalin bikin a dandalin.

Kara karanta wannan

Yanzu: Rikici ya barke tsakanin dan Shi'a da mazauna a Kano, ya jawo kone-kone

Asali: Legit.ng

Online view pixel