Bidiyo: Amarya ta hana ango ya sumbace ta don kar ya bata mata kwalliyar biki

Bidiyo: Amarya ta hana ango ya sumbace ta don kar ya bata mata kwalliyar biki

- Mata 'yan kwalisa sun daukaki kwalliya tare da bata muhimmanci a rayuwarsu

- Wata amarya ta bawa jama'ar da suka halarci bikinsu mamaki bayan ta hana angonta ya sumbaceta

- A faifan bidiyon bikin ma'auratan da ya karade dandalin sada zumunta, amaryar ta yi kememe tare da hana angonta ya sumbaceta

Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwar zamani ya nuna yadda wata amarya ta hana angonta sumbatarta saboda kar ya ɓata mata kwalliyar bikinta.

A cikin faifan bidiyon, amaryar da angonta suna shirin shiga coci cikin shigar fararen kayan ɗaura aurensa, sai suka yanke shawarar ɗaukar hotuna kafin su bar wurin.

Angon ya rungumi ƙugun amaryar tasa, sannan kuma ya kai bakinsa da zummar sumbatar ta lokacin da suka yi tsaiwar ɗaukar hoto, nan fa ta taka masa birki ta hanyar dakatar da shi da cewa "babu sumbata fa" inda ta janye jikinta daga rungumar da ya yi mata.

KARANTA: 2023: Ba zamu taba lamunta a dauki Kirista daga arewa a matsayin mataimaki ba; jigo a APC, Farfesa Mahuta

Bidiyo: Amarya ta hana ango ya sumbace ta don kar ya bata mata kwalliyar biki
Bidiyo: Amarya ta hana ango ya sumbace ta don kar ya bata mata kwalliyar biki
Asali: Original

Shi kuwa gogan yayi zaton wasa amaryar take yi masa,sai ya sake yunƙurin sumbatar amaryar, amma sai ta dage akan bakanta inda ta ce; "kawai ka yi kamar kana son sumbatata amma kar ka sumbaceni" a wannan lokacin masu kallo suka fashe da dariya.

Rahotanni sun nuna cewa Wedding Digest ne suka fara watsa faifan bidiyon, kamar yadda The Nation ta wallafa.

KARANTA: Ganau: Yadda shugaban APC na jihar Nasarawa ya yi ta ihun 'a taimaka min' kafin a kashe shi

A kwanakin baya Legit.ng Hausa ta wallafa labarin yadda wata kotun Majistire a Abuja ta bawa rundunar 'yan sanda umarnin su cigaba da tsare wani magdanci wanda ya amsa laifin gantsarawa matarsa cizo har ta kai jallin ya guntule mata ƴan-yatsu uku a hannunta.

Bayan ya amsa laifinsa, magidancin, mai shekaru 45, ya roƙi sassauci a hukuncin da alƙali zai zartar.

Ƴan sanda sun tuhumi magidanci, wanda yake zaune a ƙauyen Gui na yankin Sunka a Abuja, da laifuka nau'i biyu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng