Matar Sarki Ta Haifi ’Yan 3 Bayan Shekaru 17 Ana Jiran Haihuwa a Jihar Kogi

Matar Sarki Ta Haifi ’Yan 3 Bayan Shekaru 17 Ana Jiran Haihuwa a Jihar Kogi

  • Matar basaraken Kogi mai suna Olori Teniola-Faith ta haifi 'yan uku a ranar Litinin a asibitin koyarwa na tarayya da ke Lokoja
  • Basaraken, Oba Bologun, ya bayyana yadda yaji musamman da ya kasance matar ta sa da jariran suna cikin koshin lafiya
  • Al'ummar garin sun yi ciccirindo zuwa asibitin suna rawa da wake-wake bayan sanar da haihuwar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lokoja, Kogi - Al’ummar Apata da ke gundumar Oworo a karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi sun shiga cikin farin ciki a ranar Litinin da ta gabata.

Triplet
Sarkin ya mika godiya ga Allah kasancewar matar da yaran na shi suna cikin koshin lafiya. Hoto: Prince Adekunle Babatunde
Asali: Facebook

Farin cikin ya zo musu ne lokacin da matar sarkin garin na su ta haifi ƴan uku bayan shafe shekaru 17.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar Daso, an sanar da mutuwar wata matashiyar jarumar fina-finai

Matar sarkin, Olori Teniola-Faith, ta haifi jariran ne a safiyar ranar Litinin a asibitin koyarwa na tarayya da ke Lokoja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa al'ummar masarautar sun yi ciccirindo a asibitin suna tafi da waka da raye-raye bayan haihuwar.

Basaraken ya bayyana yadda yaji

Da yake mayar da martani bayan haihuwar, Oba Balogun ya ce:

"Wannan ita ce ranarmu ta murna da farin ciki bayan mun samu wannan kyauta mai daraja daga Allah Madaukakin Sarki bayan shekaru da dama muna jira.
"A gaskiya, ina da mai matukar mika godiya ga Allah akan abin da ya yiwa wannan gidan sarautar"

Sarkin ya kara nuna godiya kasancewar matar ta sa da jariranta guda uku duk suna cikin koshin lafiya.

A wani martanin kuma, Oba Balogun ya bayyana cewa haihuwar ƴan ukun alama ce da ke nuna cewa shekarar 2024 shekara ce ta alhairi da dama da ke tafe ga al'ummar Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Gobara ta kona dukiya mai yawa a kasuwar Balogun, 'yan kasuwa 86 sun yi babbar asara

Haihuwar 'yan hudu a Zaria

A wani labarin kuma, wata matar aure, Hauwa'u Sulaiman, ta haifi 'yan hudu a garin Zaria.

Matar ta bayyana cewa kafin haihuwar ƴan hudun, ta kasance tana da ƴaƴa 13 kuma ta ce tana cikin koshin lafiya.

Sai dai duk da kasancewar ta cikin koshin lafiyar, ta bayyana cewa an dakatar da ita a asibitin domin kara murmurewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng