Gwamnatin Tarayya Ta Nada Rahama Sadau Mukami, Ali Nuhu Ya Magantu

Gwamnatin Tarayya Ta Nada Rahama Sadau Mukami, Ali Nuhu Ya Magantu

  • Jarumar fina-finai daga Arewacin Najeriya, Rahama Sadau ta samu mukamin mamba a kwamitin shirin iDICE na gwamnatin tarayya
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya kaddamar da shirin domin tallafawa masana'antar kirkire-kirkiren abubuwan zamani
  • Legit Hausa ta zanta da Nabila Rabiu Zango, marubuciya a Kannywood, wadda ta ce Rahama Sadau ta cancanci wannan mukami

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta nada jarumar fina-finai Rahama Sadau a matsayin mamba a kwamitin gwamnati da ke kula da shirin saka hannun jari a fannin kirkire-kirkiren zamani (iDICE).

Gwamnati ta nada Rahama Sadau mukami a kwamitin iDICE
Ali Nuhu ya taya Rahama Sadau murnar samun mukami a gwamnatin Tinubu. Hoto: Rahama Sadau
Asali: Facebook

Rahama Sadau ta samu mukami

Rahama Sadau ta raba labarin nadin da aka yi mata a shafinta na Twitter, wanda wani Imran Muhammad ya wallafa.

Kara karanta wannan

"Ka mayar da Pam matsayin shugaban NCPC": Dattawan Arewa sun buƙaci Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Ibrahim Shettima ne ya kaddamar da kwamitin a ranar Laraba a Abuja.

Shirin iDICE hadin guiwa ne tsakanin gwamnati da hukumomin duniya da suka hada da bankin masana'antu, bankin raya Afrika, hukumar raya Faransa, da bankin bunkasa Musulunci.

Rahama Sadau da kwamitin shirin iDICE

Aikin shirin shi ne zakulowa tare da tallafawa mutane ko kamfanonin da suke da wata fikira ta zamani musamman a bangaren sana'o'i.

A yayin kaddamar da shirin, Shettima ya ce majalisar zartarwar Najeriya ta amince a fitar da $617.7m domin gudanar da shirin a jihohi 36 na kasar ciki har da Abuja.

An nada Rahama Sadau, Mr. Olumide Soyombo, Mrs. Kadaria Ahmed, Mr. Musa Ali-Baba da wasu a matsayin 'yan kwamitin shirin na iDICE.

Gwamnatin Tinubu ta yi abin a yaba?

Kara karanta wannan

Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah

Legit Hausa ta tuntubi Nabila Rabiu Zango, marubuciyar fina-finai a Kannywood, domin kin ta bakin ta kan wannan mukami da jaruma a masana'antarsu ta samu.

Nabila ta ce samun mukami a wajen mace kuma 'yar Arewa abu ne na farin ciki, duba da cewa gwamnatocin da suka shude ba su jawo 'yan Kannywood a jiki ba.

Marubuciyar ta ce:

"Da arziki a gidan wasu gwanda a gidanku, tabbas wannan matsayi ya nuna cewa muma 'yan Arewa ba a barmu a baya ba.
"Za mu iya cewa cancantar ta ce ta jawo mata kuma muna fatan zata tafiyar da shi yadda ya dace domin samun irin wannan matsayin tamkar ci gabanmu ne baki daya."

Ali Nuhu ya taya Rahama Sadau murna

Jim kadan bayan da aka sanar da wannan nadin, babban daraktan hukumar fina-finai ta Najeriya, Ali Nuhu ya taya Sadau murnar samun wannan mukami.

Da yake taya jarumar murna a shafinsa na Facebook, Ali Nuhu ya ce:

Kara karanta wannan

NERC ta tsokano ‘yan kwadago, ana yi wa Tinubu barazana saboda kudin lantarki

"Ina taya daya daga cikin mu murnar samun mukami a kwamitin gudanar da shirin iDICE (Investment in Digital and Creative Enterprise)."

Wannan nadin na Rahama Sadau na zuwa ne bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ali Nuhu muƙamin shugaban hukumar fina-finai ta kasa.

A halin yanzu dai Nuhu da Sadau ne jarumai daga Arewa da suke da mukami a gwamnatin APC mai mulki a kasar.

Jarumai sun taya Ali Nuhu murna

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa jaruman Kannywood, da masu shirya fina-finai har ma da 'yan bayan fage, sun taya Ali Nuhu murnar samun mukami.

Shugaban kasa Bola Tinubu ne ya nada Ali Nuhu mukamin shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.