Saurayi ya tura wa budurwa N50,000 saboda damar hira da ita da ta bashi a kafar sada zumunta
- Wani saurayi ya turawa budurwa zunzurutun kudi har naira dubu hamsin saboda kawai ta yi masa martani a sakon da ya aika mata
- Mutane sunyi caa akan saurayi da budurwar , inda wani bangaren ke cewa matan Najeriya kwadayinsu yayi yawa, wasu kuwa suna fadin akasin hakan
- Budurwar dai ta wallafa hotunan yadda ta kasance tsakaninta da saurayin
Kan mutane ya rarrabu a shafin sada zumunta na Twitter, bayan wata budurwa ta bayyana cewa wani mutumi ya tura mata kudi har naira dubu hamsin (N50,000) saboda kawai ta mayar masa da martanin sakon da ya aika mata a shafin sadarwa.
Budurwar mai suna @_Matriach da ta wallafa hotunan hirar da tayi da mutumin da kuma sakon waya da aka aika mata na kudin da ya tura mata, ta ce: "Kai ina matukar zama na mace."
Wannan rubutu da tayi ya sanya wasu maza sun tada jijiyar wuya, suka dinga zagin mutumin, akan wannan abu da yayi na turawa mace kudi domin ya jawo hankalinta.
Wasu kuma sunyi caa akan matan Najeriya akan halayyarsu ta neman kudi a wajen maza, inda suka bayyana cewa wannan dalili ne ya sanya mazan Najeriya suka fi ganewa auro matan da ba 'yan Najeriya ba.
KU KARANTA: Kaduna: Ambaliyar ruwa ta lashe rayuka 3, gidaje da yawa sun salwanta
Wani mai suna @MrOdanz cewa yayi: "Abin mamaki mutum ya turawa mace dubu hamsin saboda kawai ta bashi damar magana da ita a social midiya. Ba za a koyawa 'yan Najeriya da za su zo nan gaba irin wannan rashin hankalin ba. Dole ne wannan haukan ya mutu tare da mu."
Ita kuwa wata mai suna @1nigeriangirl cewa tayi: "Daga yaya wannan dubu hamsin da ka bayar ta sanya turawa suke turuwar sonka? Maza ka karbi Visa ka bar kasar nan.
Shi kuwa Yariman Dubai mai jiran Gado, Sheikh Hamdan bin Mohammed bin Rasha Al-Maktoum, ya nunawa duniya cewa ba komai bane idan ka zama mai adalci ga dabbobi.
KU KARANTA: Masoya sun sha maganin kwari, sun sheka lahira bayan an hana su aure
Sheikh Mohammed ya dakata da amfani da motarsa mai kirar Mercedez Benz G-Wagon saboda ya samawa tsuntsayen guda biyu wajen da za suyi sheka.
Yariman ya daina amfani da wannan mota domin ya tabbatar da lafiyar wadannan tsuntsaye.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng