Kukan Daɗi: Budurwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Samu Kyautar Maƙudan Kuɗi

Kukan Daɗi: Budurwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Samu Kyautar Maƙudan Kuɗi

  • Hausawa na cewa alheri kuikuyo ne mai shi yake bi, kuma duk mai yin sa baya faɗuwa ƙasa a banza
  • Wata budurwa ta ga ranar kyautatawa bayan wani abun kirki da tayi a baya, ya sanya ta samu kyautar maƙudan kuɗaɗe
  • Tsaɓar murna da farin ciki ya sanya budurwar fashewa da kukan daɗi bayan tayi ido huɗu da maƙudan kuɗaɗen

Wata budurwa mai suna Shelly tayi gamo da katar bayan an gwangwaje ta da kyautar maƙudan kuɗaɗe.

Budurwar dai ta samu kyautar naira miliyan goma da dubu ɗari biyar (N10.5m) daga wajen wani mai amfani da manhajar TikTok.

Budurwa
Kukan Daɗi: Budurea Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Samu Kyautar Maƙudan Kuɗi Asalin Hoto: TikTok/JimmyDarts da Bloomberg
Asali: TikTok

An tarawa budurwar kuɗin ne a yanar gizo domin yaba mata kan wani abun alheri da ta yiwa wani a mutum daban.

Lamarin ya fara ne bayan da Jimmy Darts, wani mai faɗa aji a TikTok, ya sameta a shagonta na wanki da guga sannan ya nemi da ta bashi kuɗi.

Kara karanta wannan

"Wannan Cin Mutunci Ne" Gwamna Wike Ya Ƙara Fusata, Ya Yi Wa Atiku Tatas Ana Saura Kwana 5 Zabe

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shelly ta gaya masa cewa bata da saurin kuɗi da suka rage mata domin duk ta ƙarar da su.

Sai dai domin kada ta bar shi hakanan ba tare da bashi komai ba, sai ta ɗauko sabulu daga cikin jakarta ta bashi.

Jimmy ya amshi kyautar sannan ya bata wata riga wacce ke ɗauke da tsabar kuɗi har naira dubu ɗari biyu da talatin.

Jimmy bai tsaya iya nan ba, sai da yaje ya ƙara tarawa Shelly ƙarin naira miliyan goma da dubu ɗari biyar.

Lokacin da maƙudan kuɗin suka isa hannunta, Shelly ta fashe da kukan daɗi a cikin bidiyon wanda tuni yanzu haka ya yaɗu.

A jikin bidiyon ya rubuta cewa:

"Ta bayyana cewa mahaifinta ya gaya mata cewa yana alfahari da ita bayan yayi arba da bidiyon, sannan tace bata taɓa zaton zata ji mahaifin na ta ya faɗi hakan ba."

Kara karanta wannan

Har Wani Hamami Suke: Matashi Ya Koka Kan Tsofaffin Kuɗin Da Banki Ya Ba Shi

Matashi Ya Koka Bayan Banki Ya Lafke Shi Da Takardun Tsofaffin Kuɗi

A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya koka kan rashin kyawun kuɗin da aka bashi a banki.

Ya bayyana wani irin abu da kuɗin suke da shi wanda yasa ya koka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel