A madadin yi wa budurwa 'Ramadan Basket', matashi ya sa mahaifiyarsa kukan daɗi
- Wani faifan bidiyo da ya ja hankalin mutane ya nuna yadda wani matashi ya aikawa mahaifiyarsa kyautar kudi da ya ba ta mamaki
- Mahaifiyar ta nuna matukar jin dadinta akan abin da danta ya yi ta hanyar aika masa da sakon murya mai tsuma zuciya
- A cikin sakonta mai ratsa zuciya, ta yi addu'ar ubangiji ya albarkaci aikin da danta yake yi da kuma fatan samun ci gaba a rayuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wani faifan bidiyo ya nuna irin shaukin da wani matashi ya jefa mahaifiyarsa a ciki bayan da ya aika mata kudi a matsayin kyautar watan Ramadan, al'amarin da ya dauki hankulan mutane a yanar gizo.
Mahaifiyar da ta nuna matuƙar jin dadinta kan wannan kyautar ba zata, ta aika masa da sakon murya mai tsuma zuciya.
Muhimmancin kyautatawa iyaye
A cikin sakonta mai ratsa zuciya, ta yi masa addu’ar samun nasara a dukkan al’amuransa tare da bayyana fatanta na samun ci gabansa a rayuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan labarin mai daɗi, kamar yadda @jicoblack ya wallafa a Tik Tok, ya zama abin tunatarwa ga matasa da su tuna da iyayensu a wannan lokaci maimakon aika wa budurwa 'Ramadan basket'.
Haka nan kuma yana nuna muhimmancin tunawa da na-kusa da kai domin ba su tallafi a wannan watan Ramadan, wanda zai sa ka samu tarin lada daga Allah (S.W.A).
Kalli bidiyon da ke ƙasa:
Ra'ayoyin jama'a
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a kan wannan bidiyo:
User928399373933838 ya ce:
"Ya fi kyau in bai wa iyayena kudi fiye da in bai wa budurwar da ban aura ba, Allah ya yi mahaifiyarka tsawon rai."
YEKINI ya rubuta cewa:
"Walahi wannan shi ne abin da Annabi ya bayyana a matsayin abun albarka da nasara a rayuwa. Idris Ayinde ba za ka taba kashe kuɗinka a kan rashin lafiya ba."
Cranberry2 ta ce:
"Amin, amma don Allah bai dace ace kowa sai ya san sunan mahaifiyarka ba."
Ita kuwa Temitopeoluwa716 ta rubuta:
"Wannan irin mahaifiyata ce, wasu lokutan idan ta fara yi mun addu'a sai na ce mata ta dakata haka nan. Allah ya albarkaci iyayen kwarai da 'yayansu."
Lokutan azumi a fadin duniya
A wani rahoton na daban, Legit Hausa ta yi cikakken bayani game da lokutan azumi a kasashen duniya, yayin da ake gudanar da zumin Ramadan na shekarar 1445.
Wannan rahoton zai taimaka wajen ilimantar da Musulmi kan lokutan sahur da buda baki a kasashe daban-daban da kuma wasu hukunce-hukunce da suka shafi azumi.
Asali: Legit.ng