Kamar Kano, Gwamnatin Kebbi Ta Fara Yi Wa Zawarawa Auren Gata

Kamar Kano, Gwamnatin Kebbi Ta Fara Yi Wa Zawarawa Auren Gata

  • Akalla 'yan mata da zawarawa 300 ne gwamnatin jihar Kebbi ta yi masu auren gata a ranar Lahadin da ta gabata a Birnin Kebbi
  • Gwamnatin jihar ta kashe naira miliyan 21 don biyan kowacce amarya naira dubu 70 kudin sadaki bayan yi masu kayan daki
  • Gwamnan jihar, Nasir Idris ya ce hakan zai taimaka wajen rage zawarawan da ke yawo a gari da mazan da ke son yin aure amma babu hali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kebbi - Akalla 'yan mata, zawarawa da marasa galihu 300 ne aka aurar da su ga masoyansu wanda gwamnatin jihar Kebbi ta dauki nauyin yi.

An yi daurin auren 'yan mata da zawaran ne a fadar Abdullahi Fodio da ke Masarautar Gwandu a Birnin Kebbi a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina: Ku tashi tsaye ku kare kan ku daga hare-haren 'yan bindiga

Gwamnatin Kebbi ta fara yi wa zawarawa auren gata.
Kamar Kano, Gwamnatin Kebbi ta fara yi wa zawarawa auren gata. Hoto: Yahaya Danjada
Asali: Facebook

Hajiya Nafisa Nasir Idris, uwargidan gwamnan jihar ce ta shirya daurin auren a karkashin shirinta na gidauniyar Nafisa Nasir (NANAS), bisa sahalewar gwamnatin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta rinka yin auren gata lokaci bayan lokaci

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Gwamna Nasir Idris, wanda ya jagoranci daurin auren, ya shawarci ma'auratan da su kasance abokan zaman juna na har abada.

Gwamnan ya samu wakilcin kakakin majalisar dokokin jihar, Muhammad Usman-Ankwe, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Ya bayyana cewa za a rinka gudanar da irin wannan auren gatan lokaci bayan lokaci don taimakawa marasa galihu maza da mata da ke son yin aure.

Manufar yi wa 'yan mata da zawarawa auren gata a Kebbi

Mista Idris ya ce gwamnatinsa ta bayar da naira miliyan 21 a matsayin sadaki na matan su 300 da suka fito daga kananan hukumomin jihar 21, inda kowacce amarya ta samu sadaki naira 70,000.

Kara karanta wannan

Siyasar jihar PDP ta sake rikicewa bayan hadimar gwamnan ta ajiye mukaminta, akwai dalilai masu yawa

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin ta kuma samar da kayayyakin daki da kayan abinci ga dukkan ma'auratan domin karfafa alakar aurensu.

A yayin da ya yabawa uwargidansa (Nafisa) bisa wannan namijin kokarin, gwamnan ce hakan zai rage yawan zawarawa da kuma taimaka wa mazajen da ba su da halin yin aure.

‘Yar Najeriya a UK na neman tallafin naira miliyan 17.6

A wani labarin, wata dalibar Najeriya da ke karatu a wata jami'ar kasar Birtaniya, ta nemi taimakon jama'a don karasa biyan kudin makarantarta.

A cewar dalibar, saura watanni biyar kacal ya rage ta gama makarantar, amma har yanzu ba ta samu damar kammala biyan kudin makarantar ba, har jami'ar na barazanar korarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.